Bauchi: Tsoho Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC
- Sagir Aminu Saleh, tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi da wasu kusoshin jam'iyyun adawa sun koma APC
- Masu sauya shekar sun samu tarba a hukumance daga shugaban APC, Abdullahi Adamu a wurin kaddamar da kamfe a Bauchi
- A jawabinsa na wurin taron, Adamu yace APC ta ɗauki darasi daga kuskuren da ta tafka a 2019 zata lallasa PDP a Bauchi a 2023
Bauchi - Tsohon mataimakin gwamna a jahar Bauchi, Sagir Aminu Saleh, ya sauya sheka zuwa jam'iyar APC gabanin babban zaɓen 2023.
Saleh, ya jagorancin dubbannin magoya baya daga wasu jam'iyyun siyasa zuwa APC ranar 22 ga watan Disamba, 2022, kamar yadda jaridar Tribune ta rahoto.
Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, shi ne ya tarbi dandazon masu sauya shekar a wurin kaddamar da kamfen ɗan takarar gwamnan Bauchi, Sadique Baba Abubakar.
Legit.ng Hausa ta gano cewa an gudanar da gangamin yakin neman zaben ne a filin tunawa da Abhbakar Tafawa Balewa dake Bauchi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda zamu lallasa PDP a zaben 2023 - Abdullahi Adamu
Da yake jawabi a wurin taron, Adamu ya ce Jam'iyyar APC zata kwace kujerar gwamnan jihar Bauchi a babban zaɓen 2023.
Yace APC ta ɗauki darasi bayan rasa kujerar gwamnan jihar a 2019, ya kuma jaddada cewa jam'iyyar zata yi ƙasa-ƙasa da gwamna mai ci, Bala Muhammed a 2023.
Abdullahi Adamu ya ce:
"Jihar Bauchi ta APC ce tun asali Kuma a yanzun mun kammala shirye-shirye masu kwari na kwace mulki a babban zaɓen 2023."
Bayan haka, Sanata Adamu ya roki magoya bayan APC a Bauchi da su kaɗa wa ɗan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kuri'unsu da ɗan takarar gwamnan Bauchi, Air Marshall Sadique Baba Abubakar.
A wani labarin kuma Fitaccen Malamin Musulunci Ya Shawarci Yan Arewa Kar Su Zabi Dan Takarar da Zai Murkushe 'Yan Bindiga
Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci mutane kar su zabi 'yan siyasan dake jiran su samu mulki, su sayo makamai don murkushe 'yan bindiga.
Fitaccen Malamin yace a halin yanzun ana bukatar shugaban da zai yi sulhu da yan bingida ya masu duk abinda suke so a zauna lafiya.
Asali: Legit.ng