Buhari Ya Fadawa ‘Yan Najeriya Abin da Zai Faru Idan Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa
- Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron rufe musabakar Al-Kur’ani da aka yi a jihar Zamfara
- Mai girma Shugaban Najeriyan ya aika Farfesa Isa Ibrahim Pantami ya wakilce shi ne a wajen taron
- Buhari ya yi wa mutanen Zamfara alkawarin cewa za a samu cigaba idan Bola Tinubu ya ci zabe
Zamfara - Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatarwa mutanen jihar Zamfara cewa za a ga sauyi idan Asiwaju Bola Tinubu ya dare kan karagar mulki.
Leadership ta ce Muhammadu Buhari ya nuna za a samu matukar cigaba fiye da wanda aka samu a karkashin jagorancinsa cikin tsawon shekaru bakwai.
Mai girma shugaban Najeriyan ya yi wannan bayani ne ta bakin Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami wanda ya wakilce shi wajen gasar Kur’ani da aka shirya.
Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi jawabi a gaban kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima a Gusau, a nan ya nuna sa ran APC za ta lashe zaben 2023.
Jawabin Yusuf Idris Gusau
A jawabin da Sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, an fahimci shugaban kasa ya je Gusau ne wajen musabaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kwamitin yakin zaben APC, Sanata Kabiru Garba Marafa ya zagaya da wakilin shugaban kasar a ziyarar da ya kai wajen rufe gasar shekarar nan.
A madadin shugaban kasa, Farfesa Isa Ibrahim Pantami ya ji dadin irin tarbar da aka yi masa a dalilin kokarin Gwamna Bello Matawalle da manyan 'Yan APC.
Jam'iyyar APC ta dinke a Zamfara
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin ya yaba da kokarin da tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar da Sanata Kabiru Marafa.
"Isa Pantami ya tabbatarwa mutanen jihar cewa idan Bola Tinubu ya zama sabon shugaban kasar Najeriya, kasar nan za ta samu gagarumar sauyi, za a samu cigaba daga nasarorin da aka samu a fadin kasar nan a shekaru bakwai da ‘yan kai.
Shugaban kasar ya godewa mutanen jihar Zamfara da ‘yan Najeriya a kan goyon bayan da ya rika samu a karkashin jagorancinsa tare da kira ga mutanen Najeriya su cigaba da goyon bayan APC domin ganin ta samu nasara a zabuka mai zuwa."
- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami
Pulse ta rahoto cewa shugabannin APC da sakataren gwamnatin Zamfara, tsohon gwamnan Soja da magoya bayan APC daga kasar Nijar sun halarci taron.
An ci APC tara a Ebonyi
An ji labarin yadda sabawa doka wajen yin kamfe ya jefa manyan jam'iyyun siyasa irinsu APC, PDP, LP da kuma APGA a matsala da gwamnatin jihar Ebonyi.
Gwamnatin David Umahi ta lafta tarar N5m a kan wadannan jam’iyyun siyasa, duk wanda bai biya kudin kafin 31 ga Disamba ba, tararsa za ta koma N50m.
Asali: Legit.ng