Gwamna Ya Yi Fatattaka, Ya Nada Bahaushe Ya Zama Kwamishinansa a Kuros Riba
- Gwamnan Jihar Kuros Riba ya nada wani Bahaushe a cikin wadanda za su zama sababbin Kwamishinoninsa
- Malam Adamu Uba Musa ya samu shiga majalisar zartarwar K/Riba bayan zabensa da Farfesa Ben Ayade ya yi
- A tarihin jihar Kudu maso kudun, ba a saba jin mutumin Arewacin Najeriya ya dare wata babbar kujera ba
Cross River - Abin ban mamaki aka gani a jihar Kuros Riba domin Mai girma Gwamnan Jihar, Ben Ayade, ya zabi Bahaushe a Kwamishinoninsa.
A wani rahoton Aminiya da aka fitar a ranar Asabar, 24 ga watan Disamba 2022, an ji Farfesa Ben Ayade ya nada Adamu Uba Musa ya zama Kwamishina.
Adamu Uba Musa wanda daga yankin Arewacin Najeriya ya fito, shi ne Bahaushe na farko da zai rike wannan kujera a tarihin jihar a cikin shekaru 55.
Jaridar tace ba a taba wani Bahaushen da ya rike babban mukami a gwamnatin Kuros Ribas ba. Jihar tana yankin Kudu maso kudancin Najeriya ne.
Majalisa ta amince a nada Adamu Musa
Mai girma Gwamna Ayade ya aikawa ‘yan majalisar dokokin Kuros Ribas jerin sunayen wadanda yake so a amince da su a matsayin Kwamishinoni.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Malam Adamu Uba Musa yana cikin wadanda sunayensu ya je gaban majalisar jihar, kuma ba tare da bata lokaci ba, ‘yan majalisar suka yi na’am da hakan.
Kamar yadda tsarin mulkin kasa ya tanada, sai ‘yan majalisar dokoki sun yi na’am da mutum sannan zai iya rike kujerar Kwamishina a gwamnatin jiha.
Duk wanda Gwamna ya tura sunansa da ya yi rashin dace a majalisa, ba zai iya darewa kujerar ba domin Gwamna bai da ikon da zai yi nadin shi kadai.
2023: Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Jita-Jitar Da Ake Yi Cewa Tinubu Zai Musuluntar Najeriya
Kiran Eteng Jonah Williams
Rt. Hon. Eteng Jonah Williams wanda shi ne shugaban majalisar dokokin jihar, ya yi kira ga wadanda za su Kwamishinonin su rike gaskiya da rikon amana.
A zaman ne Majalisar ta yarda a nada Dr. Janet Ekpenyong ta zama Darektan ma’aikatar lafiya.
Wanene Adamu Uba Musa?
An haifi Adamu Uba Musa ne a garin Ogoja a yankin Arewacin Kuros Ribas, hakan yana nufin duk da asalinsa na ‘Dan Arewa ne, a Kudu aka haife shi.
A yankin Ogoja Adamu Musa ya yi karatunsa na firamare da sakandare, daga nan kuma ya fi jami’ar har ya samu shaidar digirin farko a harkar mulki.
Osun: Adeleke vs Oyeyola
Kun ji labari Jam’iyyar APC tana ganin ta kanta tun da PDP ta karbe mulkin jihar Osun, Gwamnatin Ademola Adeleke ta taso Gboyega Oyetola a gaba
Ana zargin Oyetola wanda ya yi mulki All Progressives Congress da mutanensa sun dauke motocin kusan Naira biliyan uku kafin su sauka daga mulki.
Asali: Legit.ng