Da Zarar Na Sauka a Mulki, Zan Yi Nisa da Abuja Don Guje Wa Matsaloli, Inji Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai zauna a Abuja ba bayan ya gama mulkinsa a shekarar 2023
- Buhari ya ce zai nisanci Abuja saboda gujewa aukuwar wasu matsaloli, kuma zai koma Daura da rayuwa
- Ba wannan ne karon farko da Buhari yace zai koma Daura da zama ba idan ya sauka a mulki a 2023
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammad Buhari ya sake jaddada cewa, zai koma Daura ta jihar Katsina da zarar ya sauka daga mulki bayan zaben 2023 don gujewa matsaloli.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin da ya karbi bakuncin mazauna Abuja a bikin Kirsimeti, Channels Tv ta ruwaito.
Daga nan ya bayyana godiya da yabo ga 'yan Najeriyan da suka nuna yarda, goyon baya da ba shi damar shugabantarsu.
Buhari ya yi amfani da bikin na Kirsimeti wajen tabbatarwa 'yan Najeriya cewa ba zai jima ba a ofishin shugaban kasa bayan zauka daga mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma shaidawa tawagar karkashin jagorancin ministan FTC, Mohammed Bello cewa, yayin da yake kamfen a 2015, ya bi kananan hukumomi 744 na kasar don tallata manufarsa.
Hakazalika, ya ce ya samu goyon bayan 'yan kasar a lungu da sako, wanda hakan ne ya ba shi damar mulkin Najeriya.
Ya shaida cewa, ba tare da la'akari da watacciyar fasaha ba, zai zauna cikin aminci a birninsu na Daura a Katsina.
Asali: Legit.ng