Zaben 2023: Ina Da Yakinin APC Za Ta Lashe Zabe a Zamfara - Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga yan Najeriya da su zabi Bola Tinubu a zabe mai zuwa
- Buhari ya nuna yakinin cewa jam'iyyarsu ta APC mai mulki za ta lashe zabe a jihar Zamfara
- Shugaban Najeriyan ya kuma ce da Tinubu a matsayin magajinsa, kasar za ta samu gagarumin sauyi
Zamfara - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna karfin gwiwar cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki za ta yi nasara a jihar Zamfara a babban zaben 2023 mai zuwa.
Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci ofishin yakin neman zaben shugaban kasa na Tinubu/Shetima a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Pantami wanda ya kewaya ofishin da taimakon shugaban kwamitin na jihar, Sanata Kabiru Garba Marafa, ya jinjinawa tanadin da aka yi don tabbatar da nasarar jam'iyyar a jihar.
Tinubu zai kawo gagarumin sauyi a matsayin shugaban kasa
A cikin wata sanarwa da ya fitar, sakataren labaran APC a Zamfara Yusuf Idris Gusau, ya ce shugaban kasar ya baiwa mutanen jihar tabbacin cewa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu zai kawo gagarumin sauyi a kasar, rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kasar ya yi godiya ga mutanen Zamfara da daukacin yan Najeriya kan goyon bayan da suke baiwa gwamnatinsa.
Buhari ya kuma bukaci yan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan APC ta hanyar tabbatar da ganin ta yi nasara a dukkan matakai a zabe mai zuwa.
Da yake yiwa Pantami da tawagarsa maraba da zuwa, Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya ce jihar Zamfara ta APC ce, yana mai cewa jam'iyyun adawa basu da fada a jihar.
Ba zan yi kewar shugabancin Najeriya ba, Buhari
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana iya bakin kokarinsa don ciyar da kasar Najeriya gaba amma wasu basa ganin haka.
Buhari ya ce ba zai yi kewar fadar shugaban kasa ba sosai saboda kushe shi da cin zarafin da wasu yan Najeriya ke yi masa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 23 ga watan Disamba a wajen liyafar cika shekaru 80 da aka shirya masa.
Asali: Legit.ng