2023: Shugabar Matan APC a Jihar Jigawa Ta Sauya Sheka Zuwa PDP

2023: Shugabar Matan APC a Jihar Jigawa Ta Sauya Sheka Zuwa PDP

  • Shugabar matan jam'iyyar APC da ta sauka a jihar Jigawa, Hajiya Hauwa Yusuf Gumel, ta sauya sheka zuwa jam'iyar PDP
  • Ɗan takarar gwamnan jihar na PDP, Mustapha Lamido, yace za'a shirya gagarumin taro domin karɓanta a hukumance
  • Yace jam'iyyar PDP ta kowa ne a Najeriya kuma ta ɗauki mata da matasa da matukar muhimmanci

Jigawa - Shugabar matan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Jigawa, Hajiya Hauwa Yusuf Gumel, ta sauya sheka zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

Jaridar Leadership ta rahoto cewa tsohuwar shugabar matan ta ziyarci ɗan takarar gwamnan jihar a inuwar PDP, Mustapha Sule Lamido.

PDP da APC.
2023: Shugabar Matasan APC a Jihar Jigawa Ta Sauya Sheka Zuwa PDP Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Hajiya Hauwa ta samu rakiyar tsohon kwamishinan yaɗa labarai, matasa, wasanni da Al'adu a zamanin mulkin tsohon gwamna Sule Lamiɗo, Alhaji Aminu Muhammad zuwa gidan ɗan takarar.

Yayin wannan ziyara ne Mustapha Lamiɗo ya karbi Hajiya Hauwa Gumel zuwa babbar jam'iyyar hamayya watau PDP.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Yi Babban Rashi, Wani Babban Ƙusa a PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan takarar gwamnan ya tabbatarwa Hauwa da cewa ta ɗauka ta zo gida domin ba bu mai nuna mata banbanci kuma za'a bata dama da alfarmar da kowa ne mamban PDP ke da su.

Mustapha Lamido, ya kara da cewa jam'iyyar PDP zata shirya gangamin taro na musamman domin tarban Hauwa da dandazon magoya bayanta a hukumance.

Ɗan takarar gwamnan Jigawa a inuwar PDP ya faɗa wa tsohuwar shugabar matan APC, Hajiya Hauwa, cewa jam'iyyar PDP ta kowa ce a Najeriya.

"PDP a jam'iyya ce da ke kokarin kare muradan kowane ɗan Najeriya kuma tana kallon mata da matasa a matsayi mai girma," inji Mustapha Sule Lamido.

Abokin Takarar Kwankwaso Ya Faɗi Yuwuwar NNPP Ta Kulla Maja da Wasu Jam'iyyu Nan Gaba

A wani labarin kuma Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a NNPP yace sun kulle kofa game da batun kulla kawance da wasu jam'iyyu

Kara karanta wannan

Jiga-jigan APC Da Dama Sun Yi Watsi Da Tinubu, Sanwo-Olu, Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga PDP Ta Atiku, Jandor

Bishof Idahosa ya kore wani zance na kokarin NNPP na haɗa karfi wasu jam'iyyu, yace kofar jam'iyyarsu a bude take ga masu son shigowa su ba da gudummuwa.

Abokin gamin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, ya jaddada yaƙininsa cewa jam'iyyar NNPP ce zata lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262