Kotu Ta Kori Wali, Ta Tabbatar Da Abacha A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano A PDP
- Kotun tarayya a Jihar Kano ta soke zaben fidda gwani na gwamna a jam'iyyar PDP wacce ta bawa Sadik Aminu Wali nasarar zama dan takarar gwamna
- Kotun ta ayyana cewa Mohammed Sani Abacha shine halastaccen dan takarar gwamna na PDP a zaben 2023 kuma ta kori Wali biyo bayan karar da Abacha ya shigar
- Har wa yau, kotun ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC ta maye gurbin sunan Wali da na Abacha a takardan jerin sunayen yan takarar gwamna na zaben 2023
Jihar Kano - Babban kotun tarayya da ke zamanta a Kano, a ranar Alhamis, ta tabbatar da Mohammed Sani Abacha, a matsayin halastacen zababben dan takarar gwamna na PDP a jihar Kano.
A hukuncinsa, a yammacin ranar Alhami, Mai sharia A.M. Liman ya soke zaben cikin gida da jam'iyyar ta yi inda Sadik Aminu Wali ya yi nasara.
A maye sunan Wali na da Abacha, Kotu ta umurci INEC
Kotun ta kuma umurci hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta cire sunan Wali ta maye da na Mohammed Sani Abacha, rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da farko an shirya yin hukuncin ne da karfe 12.00 na rana a ranar Alhamis amma daga baya aka matsar da shi zuwa karfe 4.00 na yamma kuma aka bayar da shi da misalin karfe 5.30 na yamma.
Kotun ta amsa dukkan bukatun da mai shigar da kara ya nema a masa.
Wanda ya shigar da karar shine Mohammed Sani Abacha, yayin da wanda aka yi kara na farko itace hukumar INEC, Daily Trust ta rahoto.
Sarki Aminu Wali shine wanda aka yi kara na biyu, yayin da jam'iyyar PDP ce ta uku sai kuma Wada Sagagi shine na hudu.
Kotu ta rushe zaben cikin gida na PDP na kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya
A gefe guda, babban kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta rushe zaben cikin gida na jam'iyyar PDP na kujerar sanatan yankin Kaduna ta tsakiya domin rashin bin dokoki da ka'idoji.
Mai shari'a Muhammad Umar, alkalin kotun ya umurci jam'iyyar ta PDP ta sake yin wani zaben a cikin sati 2.
Asali: Legit.ng