2023: Zan Sanar da Ɗan Takarar Shugaban Kasan Da Zan Wa Aiki a Janairu, Wike

2023: Zan Sanar da Ɗan Takarar Shugaban Kasan Da Zan Wa Aiki a Janairu, Wike

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace jira ya kare, zai bayyana wanda zai mara wa baya a zaben 2023 a watan Janairu
  • Wike ya fara takun saka da Atiku Abubakar tun bayan zaben fidda gwanin PDP, wanda ya sha ƙasa a watan Mayu
  • Wike da sauran gwamnonin G5 sun kafe dole sai Ayu ya yi murabus sannan zasu goyi bayan Atiku

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce a watan Janairu zai bayyana sunan ɗan takarar shugaban ƙasan da zai mara wa baya a zaɓen 2023.

Channels tv tace Gwamna Wike, wanda ya bayyana matsayarsa ranar Alhamis 22 ga watan Disamba, 2022, yace zai tallata ɗan takarar da ya zaɓa a dukkan sassan ƙasar nan.

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike.
Hotunan Yada Wata Caudediyar Budurwa Ta Sauya Bayan Ta Shiga Soja Ta Ɗau Hankali Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

A cewarsa, wannan sanarwa ce ga masu cewa ya isa haka, "Sun gaji da abinda nake yi, to ku sani banma fara ba, zan bude sabon shafi a watan Janairu."

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa Yan Najeriya da Yawa Suna Ji Suna Gani Ba Zasu Kaɗa Kuri'a Ba a 2023

Da yake kaddamar da Gadar sama ta 10 da gwamnatinsa ta gina a ƙaramar hukumar Abio-Akpor a jihar Ribas, gwamna Wike ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Daga watan Janairu na shekara mai zuwa zan fara tallata wa mutanen mu wanda zasu zaɓa."
"Dukkan ku, waɗanda suka jima cikin waswasi, wadan da ke ta faɗin maganganu kala daban-daban a kaina, wasu su zage ni, ku jira kaɗan watan Janairun ya zo."
"Ba wai iya faɗa muku wanda zaku zaɓa zan yi ba, zan tsunduma yawo jiha zuwa jiha (ina masa yakin neman zaɓe) da kuma gaya wa 'yan Najeriya dalilin da zai sa su zaɓe shi kuma ba abinda zai faru."

Wike ya fara yar nuna yatsa da Atiku Abubakar ne tun bayan gama zaben fidda ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a watan Mayu, inda gwamnan ya sha ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano Ta Kawo Tsaiko A Shari'ar Ɗan China Wanda Ya Kashe Ummita

Bayan haka, Atiku ya sake watsi da Wike duk da ya zo na biyu a fafatawar zaben fidda gwani, ya ɗauko gwamna Okowa na Delta a matsayin abokin takararsa, lamarin da ake ganin ya ƙara fusata Wiike.

Wike tare da wasu takwarorinsa gwamnoni huɗu na PDP da ake wa laƙabi da G5 ko tawagar masu gaskiya sun tsaya tsayin daka dole shugaban PDP ya sauka ya ba ɗan kudu.

Sun jaddada cewa wannan ce kaɗai hanya ɗaya tilo da zata sa su mara wa Atiku Abubakar baya a zaɓen 2023.

Kwamishina a Jihar PDP Ta Yi Murabus, Ta Sauya Sheka Zuwa APGA

A wani labarin kuma Tsagin gwamna Wike ya Gamu da Cikas a ɗaya daga cikin jihohin gwamnonin G5 na jam'iyyar PDP

Kwamishinar masana'antu a jihar Abiya, Uwaoma Olawengwa, ta yi murabus daga kan muƙaminta kana ta sanar da ficewa daga PDP zuwa jam'iyyar APGA.

A cewarta, ta ɗauki wannan matakin ne a kashin kanta kuma tana hangen kyaun jihar Abiya a karkashin ɗan takarar gwamna na APGA.

Kara karanta wannan

"Ban Sani Ba Sai Daga Baya" Gwamnan Arewa Ya Umarci a Hanzarta Sakin Wanda Ya 'Zage' Shi a Soshiyal Midiya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262