Dalilin da Yasa 'Yan Najeriya Da Yawa Ba Zasu Kada Kuri'a Ba a Zaben 2023

Dalilin da Yasa 'Yan Najeriya Da Yawa Ba Zasu Kada Kuri'a Ba a Zaben 2023

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa tace wasu mutane da yawa ba zasu samu damar kaɗa kuri'a ba ranar zabe
  • INEC tace duk wanda ya zo da katin PVC amma fuskarsa ta ki ɗauka, yatsansa ya ki ɗauka ba zai yi zabe ba
  • Hukumar ta kuma gargaɗi 'yan siyasar dake sayen katunan zabe da su shiga taitayinsu

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) tace satar katin zaɓe zata haramtawa 'yan Najeriya da yawa kaɗa kuri'unsu a babban zaɓen 2023.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Hukumar INEC ta yi gargaɗi da babbar murya ga 'yan siyasan dake sayen katunan zaɓen jama'a da su shiga taitayinsu.

Hukumar zaɓe INEC.
Dalilin da Yasa 'Yan Najeriya Da Yawa Ba Zasu Kada Kuri'a Ba a Zaben 2023 Hoto: thenation
Asali: Getty Images

A cewar INEC duk masu sayen katunan zaɓen mutane da wata manufa su sani suna ɓata lokacinsu, karfinsu da kuɗaɗensu ne a banza.

Kara karanta wannan

2023: Abokin Takarar Kwankwaso Ya Faɗi Yuwuwar NNPP Ta Kulla Maja da Wasu Jam'iyyu Nan Gaba

Kwamishinan wayar da kan jama'a da hulda da jama'a na INEC ta kasa, Festus Okoye, ne yayi wannan furucin yayin da yake jawabi a wurin taro a Ibadan, babban birnin Oyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a taron, wanda kungiyar yan jarida (NUJ) tare da haɗin guiwar INEC ta shirya, Okoye yace fasahar zamani ta taimaka wajen dakile cin zalin zaɓe da sayen kuri'u.

A cewarsa, a yanzun INEC na aiki ne da tambarin yatsan halintar mutum da kuma hoton fuska, hakan ya sa da wuya wani ya iya sojan gona a madadin wani.

Abinda zai sa a hana mutum zaɓe a 2023

"Idan sharcen yatsanka bai ɗauka to dole fuskarka tai kama da kai. Idan kuma yatsan bai daidai ba kuma fuska ma haka, to ba zaka kaɗa kuri'a ba domin hakan na nufin ba Katin zabenka bane."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Jiha Wuta, Sun Tafka Ɓarna

- Festus Okoye.

Kwamishinan, wanda ya sami wakilcin daraktan sashin jinsi, Ndidi Okafor, yace duk wanda ke zuwa yana sayen katunan zaɓen Jama'a to ya shiga adashen da babu ɗiba.

Okoye ya bayyana cewa 'yan jarida na taka rawa a kokarin gina dimokuradiyya, saboda haka akwai bukatar su kara samun horo a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar babban zaɓe.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta maida martani kan kalaman PDP game da kai hare-hare ofisoshin INEC a wasu sassan ƙasar nan

Kakakin kwamitin yakin neman zaɓen Tinubu/Shettima, Festus Keyamo, yace ya kamata hukumonin tsaro su titsiye PDP ta faɗi waɗanda ke ɗaukar nauyin kai hari Ofishin INEC.

Idan baku manta ba jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa jam'iya mai mulki ce ke kitsa waɗannan hare-haren saboda wata manufa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel