2023: Wani Babban Jigon PDP A Jihar Delta Ya Mutu A Hanyar Zuwa Taron Kamfe
- Wani jigon jam'iyyar PDP a jihar Delta, Chief Onuame, ya mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a titin Ughelli zuwa Patani
- Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da mutumin ke hanyar zuwa taron kamfe a garin Patani tare da Direbansa
- A jiya Talata wasu Kwale-kwale biyu ɗauke da mambobin APC suka yi hatsari a jihar Delta, mutane biyu suka mutu
Delta - Wani babban jigon jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Ughelli ta kudu, jihar Delta, Chief Joe Unuame, tare da Direbansa sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su da safiyar Laraba.
Jaridar Tribune ta tattaro cewa bakar Motar Jeep ta Chief Onuame ta yi taho mu gama da Babbar Tankar dakon man Fetur a bayan mahaɗar titunan Umeh a hanyar Ughelli zuwa Patani.
Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya haɗa da jigon ne yayin da yake kan hanyar zuwa taron gangamin yakin neman zabe a garin Patani.
An ce Diraban ya mutu nan take ko shurawa bai yi ba yayin da aka hanzarta kai Chief Onuame Asibiti ma fi kusa don ceto rayuwarsa amma rai ya yi halinsa a hannun Likitoci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanene Chief Onuame?
Marigayi Chief Onuame ɗan asalin garin Akpere-Olomu ne dake yankin Masarautar Olomu, ƙaramar hukumar Ughelli a jihar Delta.
Har zuwa rasuwarsa marigayin ya kasance mamba mai kishin PDP kuma ɗan gani kashenin Honorabul Sheriff Francis Orohwedor Oborevwori, ɗan takarar gwamnan Delta a 2023 na PDP.
Idan baku manta ba a jiya Talata aka samu hatsarin taho mu gama na wasu Kwale-kwale biyu na yan kasuwa a jihar Delta, mutane biyu suka rasa ransu
Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne bayan gangamin yakin neman zaben ɗan takarar gwamna a inuwar APC na gunduma-gunduma da ya gudana a Okerenkoko, ƙaramar hukumar Warri ta kudu maso yamma.
A wani labarin kuma Tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP a Jihar Oyo Ya Rasu Yana Da Shekaru 62
Jigon siyasan ya cika ne a Asibitin jami'ar jiha dake Ibadan, babban birnin jihar Oyo ranar Laraba 21 ga watan Disamba, 2022.
Kakakin PDP na jihar, wanda ya tabbatar da rasuwar yace marigayin mutum ne mai saukin kai kuma ba shi da damuwa a rayuwarsa.
Asali: Legit.ng