Jirgin Ruwa ya Tafka Hatsari, Ya Nitse da 'Yan APC 5 da Suka Fita Kamfen

Jirgin Ruwa ya Tafka Hatsari, Ya Nitse da 'Yan APC 5 da Suka Fita Kamfen

  • Jirgin ruwa ya tafka hatsari da mambobin jam’iyyar APC tare da magoya bayansu inda ake kyautata zaton rasa rayukan mutum biyar daga cikinsu
  • An gano cewa mambobin APC a jihar Deltan zuwa dawowa ne daga kamfen din Omo-Agege, mataimakin shugaban majalisar dattawa inda jirgin ruwan ya nitse
  • An samu ceto mutum bakwai wadanda yanzu haka suke asibiti yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum biyu sai mutum uku da har yanzu ba a tsamo su ba

Delta - Mambobi jam’iyyar APC biyar a jihar Delta sun sheka lahira sakamakon hatsarin jirgin kasa da ya faru a daren Talata a Rafin Gbaramatu-Warri.

Omo Agege
Jirgin Ruwa ya Tafka Hatsari, Ya Nitse da 'Yan APC 5 da Suka Fita Kamfen. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Wasu a halin yanzu suna asibiti inda suka karbar taimakon masana kiwon lafiya sakamakon raunikan da suka samu.

Jaridar Punch ta tattaro cewa, hatsarin jirgin ruwan ya ritsa da mambobin jam’iyyar APC da magoya bayansu yayin da suke dawowa daga ralin ‘dan takarar gwamnan da aka yi a Okerenkoko da Ugborodo a karamar hukumar Warri ta kudu maso yamma.

Kara karanta wannan

Gwamna Matawalle Ya Faɗi Gaskiyar Abinda Ya Faru Har Jirgin Soji Ya Kashe Mutane a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa, jirgin ruwa na haya ne ya fadawa jirgin ruwan dake dauke da magoya bayan APC din, lamarin da yasa ya nitse.

A take mutum biyu suka mutu yayin da ruwa ya tafi da wasu uku inda wasu bakwai ke asibiti suna fama da jinya.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma ‘dan takarar gwamna a APC na jihar Delta, Sanata Ovie Omo-Agege, yayin bayyana damuwarsa kan lamarin, yayi addu’ar gafara ga mamatan.

Channels TV ta rahoto cewa, wata takarda da Ima Niboro, daraktan tawagar kamfen din ‘dan takarar gwamnan jihar Deltan, wanda aka bayyana kwafinsu ga manema labarai a Warri a ranar Laraba, yace:

“Mun matukar girgiza kan wannan abun alhinin kuma zukatanmu sun yi nauyi.
“Addu’o’inmu da tunaninmu suna tare da wadanda lamarin ya ritsa dasu da iyalansu. Wannan abun alhini ne ga jama’a da yawa kuma jam’iyyar mu tana cikin makoki.

Kara karanta wannan

Borno: Boko Haram Sun Kai Hari, Sun Kone Gidaje 7, Kayan Abinci da Dabbobin Jama’a

“Muna aiki yanzu haka da hukumomin da suka dace domin ceto wadanda suka bace. Muna kuma cigaba da neman iyalai da masoyan wadanda lamarin ya ritsa dasu yayin da muke kokarin tabbatar da cewa marasa lafiyan suna samun kular da ya dace.
“Domin karrama wadanda suka rasa rayukansu, bacewa ko samun rauni, mun yanke hukuncin dakatar da kamfen har sai Baba ta gani.
“Kungiyar kamfen zata bada shawari kan abinda ya dace a yi a cikin kwanaki masu zuwa da makonni.
“Har ila yau, muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda lamarin ya shafa tare da fatan Allah ya basu hakurin jure rashin a wannan lokacin jarabawa.”

Ba a samu kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edgar har yanzu ba a waya ba don yin tsokaci kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel