2023: Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Jita-Jitar Da Ake Yi Cewa Tinubu Zai Musuluntar Najeriya

2023: Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Jita-Jitar Da Ake Yi Cewa Tinubu Zai Musuluntar Najeriya

  • Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya sake yin karin haske kan jita-jitar da ake yadawa cewa Tinubu zai musuluntar da Najeriya
  • Masari ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasar na APC, duk da zabin abokin takararsa musulmi, yana nufin alheri ne ga Najeriya da yan Najeriya
  • Hakazalika, Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce Tinubu zai maimaita abin da ya faru a zaben 1993 da aka soke

Kaduna, Kaduna - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi watsi da jita-jitar cewa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu zai musuluntar da Najeriya.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Masari ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata, 20 ga watan Disamba, yayin taron jin ra'ayin mutane tare da kungiyar kiristoci na arewa lokacin da matar Tinubu, Sanata Remi Tinubu, ta tarbe su a Kaduna.

Kara karanta wannan

2023: Sarkin Katsina Ya Faɗi Wanda Zai Iya Zama Shugaban Kasa Yayin da Ya Karbi Bakuncin Atiku

Asiwaju Bola Tinubu
2023: Fitaccen Gwamnan Arewa ya magantu kan jita-jitar da ake yi cewa Tinubu zai Musuluntar Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa ko makaho zai zabi Tinubu idan aka jera shi da sauran yan takarar shugaban kasa a yayin da ya ke karyata jita-jitar.

Gwamna Masari ya ce:

"Ba bu dalilin da za a rika tsoron cewa Tinubu zai musuluntar da Najeriya. Ba gaskiya bane. Shin Buhari ya musuluntar da Najeriya bayan shekaru bakwai a ofis? Obasanjo ya kiristar da Najeriya bayan shekaru takwas a ofis? Jonathan ya mayar da Najeriya kasar kirista bayan shekaru shida a ofis?"

Zaben shugaban kasa na 2023: Gwamna Ganduje ya yi hasashen nasara ga Tinubu

Cikin wadanda suka halarci taron akwai Gwamna Abdullahi Ganduje inda ya ce tarihi zai maimaita kansa inda ya bada misalin zaben 1993 da MKO Abiola ya yi nasara duk da kasancewarsa musulmi kuma ya zabi abokin takara musulmi, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Yan Takaran Jam'iyyar NNPP a Jihar Osun Sun Yi Watsi Da Kwankwaso, Sunce Tinubu Zasu yi

Ya ce:

"Tarihi zai maimaita kansa. Lokacin mulkin soja karkashin Janar Ibrahim Babangida yayin mika mulki ga farar hula, an yi zabe tsakanin MKO Abiola da Alh. Bashir Tofa na SDP da NRC.
"Abokin takarar Abiola musulmi ne. Tikitin musulmi da musulmi ne kuma suka ci zaben. Tofa ya zabi kirista a matsayin abokin takara kuma ya fadi zabe. Domin haka, Tinubu zai ci zaben."

A bangare guda, matar Tinubu, Sanata Oluremi, ta jadada cewa mijinta na nufin Najeriya da alheri yayin da ta ke kira ga yan kasar su zabi Jagaban, kamar yadda ake kiran mijinta.

Mukaman da kiristoci ka iya samu a gwamnatin Bola Tinubu

A bangare guda, yayin da wasu ke cigaba da nuna kin amincewarsu da tikitin musulmi/musulmi da APC ta yi, matasan kiristocin Kaduna karkashin kungiyar 'Christian Youth Movement for Tinubu/Shettima' sun bayyana kujerun da kirista za su iya mora a karkashin gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Ya Jingine 'Dan Takarar Jam'iyyarsa, Yace Tinubu Zai Wa Aiki a 2023

Idan ba a manta ba, daukan tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takara ya janyo wa Tinubu suka musamman daga kiristoci na arewa da kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164