Zaben 2023: Kotu Ta Kori Shugaban Jam'iyyar Siyasa A Najeriya

Zaben 2023: Kotu Ta Kori Shugaban Jam'iyyar Siyasa A Najeriya

  • Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta kori shugaban jam'iyyar ADC na kasa, Cif Ralph Nwosu
  • Mai shari'a Binta Nyako ce ta karanto hukuncin kotun yayin shari'ar da aka yi a ranar Talata 20 ga watan Disamba
  • Bisa umurnin da kotun ta bada a ranar Talata, ADC za ta gudanar da sabon gangami don yin zaben shugaban jam'iyya na kasa da mambobin NWC

FCT, Abuja - Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta cire shugaban jam'iyyar African Democratic Congress, ADC, na kasa, Cif Ralph Nwosu, da shugabannin jam'iyyar daga ofisoshinsu.

Kotun ta fatattaki Nwosu a cikin umurnin da ta bada a ranar Talata, 20 ga watan Disamba, yayin shari'ar da Mai Shari'a Binta Nyako ta yi.

Nwosu
Zaben 2023: Kotu Ta Kori Shugaban Jam'iyyar Siyasa A Najeriya. Photo: Chief Ralph Okey Nwosu
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Daraktan Yakin Neman Zaben Peter Obi Zaiyi Zabe A Kurkuki, Sakamakon Umarnin Kotu Na A Tsareshi

Bugu da kari, kotun ta hana Nwosu tsawaita wa'adinsa bayan karewarta bisa tanadin kundin tsarin mulki na jam'iyyar ADC, This Day ta rahoto.

Kazalika, kotun ta soke dukkan hukunce-hukunce da shugabannin jam'iyyar suka yi tun daga ranar 21 ga watan Agusta har zuwa yanzu.

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne biyo bayan karar da wani Kingsley Temitope Ogga da wasu masu mutane suka shigar a kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1541/2022.

Kamar yadda kotu ta bada umurni, jam'iyyar ta ADC za ta yi sabon gangami domin yin zaben kujerar ciyaman na kasa da mambobin kwamitin gudanarwa wato NWC.

Komawar wata sanata zuwa jam'iyyar PDP ya sa APC ta kori shugaban matasa

A wani rahoton kun ji cewa an tsige shugaban matasa na jam'iyyar APC, Innocent Nwanwa a jihar Anambra.

Nwanwa, ya kasance dan gani kashenin sanatan yankin Anambra ta Arewa kuma tsohuwar ministan sufurin jiragen sama, Stella Oduah ne, wacce ya fita daga APC ta koma PDP.

Kara karanta wannan

Yan Takaran Jam'iyyar NNPP a Jihar Osun Sun Yi Watsi Da Kwankwaso, Sunce Tinubu Zasu yi

A cewar rahoton Punch, wata majiya ta nuna cewa akwai yiwuwar sauya shekar da Oduah ta yi zuwa PDP ne yasa APC ta zartar da wannan lamarin kan shugaban matasan.

Oduah ta shigo jam'iyyar APC ne ana daf da zaben gwamnan Anambra a shekarar 2021, amma kuma a wani abu mai ban mamaki, Sanatan ya koma PDP sannan ta samu tikitin yin takarar sanata a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164