Duk Wani Ci Gaba da Aka Samu a Katsina Gwamnatin PDP Ne Ta Samar Dashi, Inji Atiku
- Dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya ce babu wani aiki da APC ko wata jam’iyya ta taba yi a Katsina
- Atiku Abubakar ya ce, duk wani ci gaba da aka samu a Katsina ya samu sanadiyyar mulkin PDP na tsawon lokaci
- Atiku ya yi alkawarin kawo karshen matsalolin tsaro a Najeriya, musamman jihohin Arewa maso Yamma
Jihar Katsina - Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya ya ce duk wani ci gaba da aka samu a Katsina dalilin gwamnatocin PDP ne, TheCable ta ruwaito.
Dan takarar na shugaban kasan a jam’iyyar PDP ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai gangamin kamfen dinsa jihar Katsina a ranar Takata 20 ga watan Disamba.
Idan baku manta ba, marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’dua ya yi mulki a jihar Katsina tun shekarar 1999 zuwa 2007, kuma a karkashin jam’iyyar PDP kafin daga bisani a zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Ibrahim Shema ne ya gaji Yar’Adua a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, wanda daga bisani ya danka ma Aminu Bello Masari, gwamnan APC na farko tun 1999.
PDP ne ya ciyar da jihar Katsina gaba
Atiku Abubakar ya ce, dukkan wasu cibiyoyi na gwamnatin jihar, ciki har da sabon gidan gwamnatin Katsina, duk PDP ne ta gina su.
A cewarsa:
“Abin da nake son shaida muku gaba daya a wannan lokacin shine, idan kuka duba, dukkan wani ci gaba da aka samu a Katsina a yau, gwamnatin PDP ne ta samar dashi.
“Ko ba haka bane? Wannan wurin ma PDP ne ta gina shi ko da kuwa tituna PDP ne ta gina su. Dukkan cibiyoyin ci gaba – babu abin da PDP bata yiwa jihar Katsina ba.
“Don haka, lokacin sauyi ya zo. Ku bar sauran jam’iyyu ku zo cikin PDP.”
Alkawarin da Atiku ya yiwa ‘yan Katsina
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kuma bayyana cewa, idan aka zabe shi zai kawar da batun ‘yan bindiga da suka addabi al’ummar yankin, Vanguard ta ruwaito.
Ya kara da cewa:
“Mun yi wani alkawari – yana daga cikin manufofinmu guda biyar da muka alkawarta da yardar Allah idan kuka zabe ni.
“Matsalar rashin tsaro zata kau kuma za a samu zaman lafiya. Mun yi alkawarin gyara tattalin arzikin kasar nan kuma za mu bude iyakokin Najeriya.
“Ina godiya a gareku duk bisa goyon bayan da kuka nuna mini, kuma ina fatan za ku zabi PDP a zabe mai zuwa.”
A gangamin kamfen na Katsina Atiku ya ziyarci mahaifiyar marigayi Yar'Adua da kuma sarkin Katsina.
Asali: Legit.ng