Bidiyon Lokacin Tinubu Ya Ba Wani Mutum Tsabar Kudi a Abuja Ya Jawo Cece-Kuce

Bidiyon Lokacin Tinubu Ya Ba Wani Mutum Tsabar Kudi a Abuja Ya Jawo Cece-Kuce

  • 'Yan Najeriya a kafar sada zumunta sun yi martani bayan da aka ga wani bidiyon lokacin da Tinubu ke ba da kyautar kudi ga wani
  • Wani bidiyo ya nuna lokacin da Tinubu da Shettima ke tattaunawa da wani dattijo a Abuja, Tinubu ya bashi kudi
  • Ana ci gaba da cece-kuce a Najeriya kan ci gaba da yawaita kashe tsabar kudi, ga shi kuma an bugo sabbin kudade

FCT, Abuja - Wani bidiyo ya yadu a kafar sada zumunta na yadda dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ba wani dattijo tsabar kudi a wurin taro.

Tinubu ya ba mutumin kudin ne a lokacin da yake ganawa da 'yan Najeriya nakasassu a babbarnin tarayya Abuja.

A bidiyon da Legit.ng Hausa ta samo daga shafin Twitter na Punch, an ga lokacin da mutumin ke zaune tsakanin Tinubu da abokin takararsa; Kashim Shettima a wurin taron yayin da mai jawabi ke magana.

Kara karanta wannan

Bakon Biki Ya Gwangwaje Amarya da Ango da Daurin Itace, Bidiyon Ya Ba Jama'a Mamaki

Bidiyon Tinubu na ba wani dattijo kudi
Bidiyon Lokacin Tinubu Ya Ba Wani Mutum Tsabar Kudi a Abuja Ya Jawo Cece-Kuce | Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Tinubu da Shettima sun saka mutumin a tsakiya suna magana dashi, kafin daga bisani dan takarar na APC ya damka masa kudi a hannu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jama'a sun yi martani

Wasu mutane a kafar sada zumunta sun shiga mamakin dalilin da zai sa ya ba da kudi haka a hannu, wasu kuma sun ce ba laifi bane ba da kyautar kudi tsaba ga mutane.

Kalli bidiyon:

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa:

@Malc_OE yace:

"Wannan kyautatawa nakasasshe kenan. Wannan mutumin ya ba da tallafi ga miliyoyin mabukata a bangarori daban-daban na kasar nan. Allah ya masa albarka bisa wannan kyautatawa."

@thisweek_ngtv yace:

"Da yawan 'yan a mutun Obi a nan sai kuka suke. Idan da Peter Obi ne ya yi haka, za sui ta yaba masa, su ce shi mutumin kirki ne, amma da ke Tinubu, sai zagi suke. Kawai ya ba dattijo kudi ne, ba cin hanci ba, cin hanci a ina."

Kara karanta wannan

Yadda Al'umma Suka Hadu Suke Gasar Cin Abinci a Jihar Cross - RIver

@femyek yace:

"Bayan ganawa da dattijo mai nakasa, ya nuna karamci ta hanyar ba shi kudi. Wannan kyautatawa kenan."

@BoakaiOgbonnaya kuwa cewa ya yi:

"Tinubu barawo."

@ekene_snr yace:

"Kuma kamar N1000 nan dai da babu ita a banki yanzu, kawai kallon Emefiele nake da ka'idojinsa."

@abusaniJoker yace:

"Wannan ba sabon kudi bane? Daidai da abin da nake fadi kenan. BAT/APC sun samu mota cike da sabbin kudade tun tuni."

Bincike ya nuna 'yan Najeriya sun fi son biyan kudi ko siyayya da hanyoyin zamani fiye da na kashe tsabar kudi a fadin kasar, inji bayanan NIBSS a 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.