Zaka Yi Samun Nasara a Burinka Na Zama Shugaban Kasa, Sarkin Katsina Ga Atiku
- Sarkin Katsina ya faɗa wa Atiku Abubakar cewa mai yuwuwa ya samu nasarar cika burinsa na zama shugaban kasa
- Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya karɓi bakuncin ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP wanda ya kai masa ziyara har fada
- Atiku ya jajantawa Sarkin bisa rashin mutane da dama sanadin rashin tsaro, ya ba da tallafin miliyan N50m
Katsina - Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya yaba wa ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
Sarkin ya yi kalaman yabon ne yayin da ya karɓi bakuncin tsohon mataimakin shugaban ƙasan a fadarsa lokacin da ya je kai gaisuwa gabanin zarcewa wurin kamfe.
Tribune Online ta rahoto cewa Atiku ya kaddamar da fara yakin neman zaben PDP na shiyyar arewa maso yammacin Najeriya a Katsina ranar Talata.
Da yake jawabi, Sarkin Katsina ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Akwai haske, mai yuwuwa ka cimma nasara a kudirinka na zama shugaban kasa. Ƙasar nan cike take da matsaloli, rashin tsaro, talaka ya rasa ɗan abinda zai sa a baki, ba wancan, ba wannan adadin bai da iyaka."
"Ba ranar da zata wuce baka samu labarin an yi garkuwa da mata ba ko kuma wani ya mutu sanadin 'yan ta'adda a yankin Masarautar Katsina."
Abdulmumini Kabir Usman ya kara da cewa suna ta Addu'a a waje ko a ɓoye domin Allah ya kawo jagoran da zai magance waɗannan matsalolin.
Atiku ya jajantawa Sarkin tare da Tallafin kudi
Tun da farko, Atiku Abubakar ya yi wa Sarkin ta'aziyyar mutanen da suka mutu sakamakon rashin zaman lafiya kana ya yi alkawarin bayar da miliyan N50m domin tallafa wa yan gudun hijira.
A wurin gangamin kamfen kuma, Atiku ya shaida wa dandazon al'ummar da suka taru cewa idan ya ci zaɓe zai aiwatar da dabarun kawo karshen ayyukan yan ta'adda a ƙasar nan.
Yace zai shawo kan matsalar rashin wutar lantarki, inda ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen rage yawaitar zaman kashe wando wanda ke haifar da aikata muggan laifuka.
Abinda Shugaba Buhari Ya Fada Wa Shehunnan Tijjaniya da Suka Kai Masa Ziyara a Aso Villa
A wani labarin kuma kun ji cewa Manyan shugabannin Jam’iyyatu Ansaridden (Attijaniyya) sun ziyarci Shugaba Buhari a Abuja
Yayin wannan ziyara ne shugaban kasan ya yaba musu kana ya gaya musu ya kosa ya koma mahaifarsa Daura idan wa'adinsa ya kare a 2023.
Shehunnan Malaman sun yi nasiha tare da jan hankali kan koyi da rayuwar Annabi Muhammad SAW.
Asali: Legit.ng