Atiku Ya Je Jihar Shugaban Kasa, Sarkin Katsina Ya Yi Magana a Kan Takararsa a PDP
- Sarkin Katsina, Dr. Abdulmumin Kabir Usman ya karbi tawagar Atiku Abubakar cikin karramawa
- Mai martaba Abdulmumin Kabir Usman ya ce akwai haske a neman mulkin da Atiku yake yi a PDP
- Basaraken ya ji dadin jawabin Wazirin Adamawa, ya yabi alakar da ke tsakanin shi da Katsinawa
Katsina - Mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmumin Kabir Usman ya yi wa Alhaji Atiku Abubakar da ‘yan tawagarsa kyakkyawar tarba a fadarsa.
A ranar Talata, 20 ga watan Disamba 2022, Atiku Abubakar mai neman zama shugaban Najeriya a 2023 ya je fadar Mai martaba Sarkin Katsina.
Vanguard ta fitar da rahoto cewa Dr. Abdulmumin Kabir Usman ya nuna akwai alamun nasara a neman shugabancin da Atiku Abubakar yake yi.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriyan ya nemi Sarki ya tofawa takarar da yake yi albarka.
Babu ruwan Sarki da siyasa
Mai martaban ya karbi Atiku da mutanensa hannu biyu-biyu, amma ya ce babu wani abin da zai iya yi masu illa addu’a domin shi ba ‘dan siyasa ba ne.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da ya saurari Atiku, Abdulmumin Kabir Usman ya koka da cewa jiharsa ta Katsina ta na cikin inda matsalar rashin tsaro ya fi yin kamari sosai a Najeriya.
Uban kasar ya nuna ya ji dadin yadda ‘dan takaran shugabancin kasar ya yi alkawarin magance manyan matsaloli biyun da suka dabaibaye su.
‘Dan siyasar ya ce idan ya samu mulkin kasar nan a Mayun shekara mai zuwa, zai kawo zaman lafiya, sannan ya bunkasa halin tattalin arzikin kasa.
Atiku mutumin Katsinawa ne
An rahoto Abdulmumin Usman yana cewa babu shakka Atiku ya dauki tsawon lokaci yana hada kyakkyawar alaka tsakaninsa mutanen Katsina.
Idan za a tuna, Marigayi Matawallen Katsina, Shehu Musa ‘Yar’adua shi ne wanda ya shigo da Wazirin Adamawa harkar siyasa shekaru fiye da suka wuce.
Wadanda suka yi wa tsohon mataimakin shugaban kasan rakiya sun kunshi Dr. Ifeanyi Okowa, shugaban PDP na kasa da sauran jagororin jam’iyyar.
Sauran ‘yan tawagar PDP da aka je fadar Sarkin da su sun hada da Gwamnonin Akwa Ibom da Sokoto, da tsofaffin Gwamnonin jihohin Neja, Kano, Jigawa.
Atiku ya bada N50m
Rahoto ya nuna ‘Dan takaran PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya bada gudumuwar Naira Miliyan 50 ga wadanda rashin tsaro ya shafa a jjihar Katsina.
Alhaji Atiku Abubakar ya bada N50m da aka yi ambaliya a Jigawa da Bayelsa, haka ya lale wadannan kudi da gobara ta yi barna a wata kasuwa a Kano.
Asali: Legit.ng