Hausawa Da Fulani Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Ayade Da APC A Jihar Kudancin Najeriya

Hausawa Da Fulani Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Ayade Da APC A Jihar Kudancin Najeriya

  • Al'ummar hausawa da fulani mazauna karamar hukumar Ogoja a Cross Rivers sun ce suna goyon bayan takarar sanata na Gwama Ben Ayade
  • Sarki Adamu, jagoran al'ummar hausawa da fulani ya ce sun yanke shawarar goyon bayan Ayade ne saboda ba ya nuna banbancin kabilanci ga mazauna jihar
  • A cewar Sarki Adamu, Ben Ayade masoyin dukkan yan Najeriya kuma ya gode masa saboda kin saka hannu kan dokar hana kiwo a fili a jiharsa

Cross Rivers - Hausawa da fulani da ke zaune a yankin Ogoja a jihar Cross Rivers sun bayyana goyon bayansu ga takarar sanata na Gwamna Farfesa Ben Ayade.

Gwamnan wanda ya wakilci Cross Rivers a majalisar dattawa a 2011 da 2015 shine dan takarar sanata na APC a zaben 2023, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Sunayen Fitattun 'Yan Siyasa 8 na Najeriya da Suka Rasu a 2022

Hausawa da fulani a Cross Rivers
Hausawa Da Fulani Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Ayade Da APC A Jihar Kudancin Najeriya. Hoto: Voice of Nigeria
Asali: Facebook

Da ya ke jawabi yayin ziyarar nuna goyon bayan ga gwamnan a jiya, mazauna unguwar karkashin jagorancin Sarki Yakubu Adamu, sun sha alwashin bada dukkan kuri'unsu ga APC daga sama har kasa.

A cewarsa, rashin nuna kabilanci na Ayade shine yasa ya zama dan takarar da hausawa da fulani za su zaba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sarki Adamu ya ce:

"Muna goyon bayan ka kuma za mu zabe ka a matsayin sanata. Kai ne dan takarar mu saboda baka nuna banbanci tsakanin kowanne dan Najeriya; ka nuna kauna ga Hausawa da Fulani a Cross Rivers.
"Za mu zabe ka a matsayin sanata kuma za mu zabi dukkan sauran yan takarar APC a zabe mai zuwa."

Ya yaba wa gwamnan kan rashin rattaba hannu kan dokar hana kiwo a fili wanda ya ce cikas ne ga halastaciyyar sana'ar makiyaya fulani, rahoton VON.

Kara karanta wannan

Haba, haba: Tinubu ya jawo cece-kuce, ya ce ana hada 'Hand Sanitizer' da masara

Martanin Ayade

A bangarensa, gwamnan ya gode wa mutanen garin bisa ziyarar da suka kawo masa da goyon bayan takararsa na sanata.

Ya ce hakan babban hujja ne da ke nuna cewa banbancin addini ba zai iya raba kan yan Najeriya ba.

Wani sashi na jawabinsa na cewa:

"Idan an haifa ka nan, ka girma a nan, ko kai Ibo ne ko bahaushe ko fulani ko bayarabe, a wuri na, kai dan Cross Rivers ne."

2023: Osita Okechukwu ya ce Peter Obi ne ke tayar wa Tinubu hankali

A wani rahoton, Jigon jam'iyyar APC, Osita Okechukwu ya ce jam'iyyar Labour Party da Peter Obi dan takarar shugban kasa na jam'iyyar ne zai iya fito na fito ta Asiwaju Bola Tinubu na APC.

Osita ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin shirin The Morning Show na Arise TV.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164