Shugaba Buhari Ya Tabbatar Mun Za'a Yi Sahihin Zabe a 2023, Atiku
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya nuna karfin gwiwar lashe babban zaben kasar da za a yi a shekara mai zuwa
- Atiku ya bayyana cewa sau biyu Shugaban kasa Buhari na bashi tabbacin gudanar da sahihin zabe a 2023
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce zai yi wuya a iya magudi a zabe mai zuwa saboda irin matakan da aka tanada
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yana da yakinin lashe zaben shugaban kasa na 2023 saboda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi tabbacin sahihin zabe.
Tsohon mataimakin shugaban kasar a wata hira da jaridar Financial Times (FT) na Landan, ya ce ya hadu da shugaba Buhari sau biyu a kan lamarin.
Atiku ya ce:
"Musamman shugaban kasar ya yi mun alkawari, saboda na zauna da shi sau biyu, cewa koda wannan ne kadai tarihin da zai bari, zai tabbatar da ganin ya gudanar da sahihin zabe na gaskiya."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Atiku ya kuma bayyana cewa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023, yana shirin kafa gwamnati mai cike da hadin kai da za ta yi hadaka da abokan adawa.
Da aka tambaye shi ko akwai aikin da za a ba dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, wanda ya kasance abokin takararsa a 2019, Atiku ya amsa da: "Me zai hana?"
Da aka tambaye shi a wani mataki, dan takarar shugaban kasar na PDP ya ce: "A bari a lashe zaben kafin a fara tunanin rawar ganin da mutane za su iya takawa."
An yi magudi a zaben 2019, Atiku
Jaridar ta kuma ce har yanzu Atiku na jin zafin kayen da ya sha a 2019, zaben da mutane da dama suka yi tsammanin zai kasance na kut da kut amma sai Buhari ya bashi tazarar kimanin kudri'u miliyan hudu, wanda hakan yasa akwai tazara sosai a tsakaninsu.
Sai dai Atiku ya dage cewa an yi magudi ne a zaben shugaban kasar na 2019 don Buhari ya ci.
Ya ce:
"Dukkanin majiyoyi da aka sanarwa yadda abun yake sun yarda cewa an yi mun magudi ne."
Atiku ya kara da cewar zai yi wuya ayi magudi a zaben 2023 saboda sauye-sauyen da hukumar zabe ta kawo ciki harda tura sakamakon zabe ta na'ura wanda yayi tasiri a zaben gwamnan da aka yi a baya-bayan nan, rahoton Leadership.
Na lashe zabe a kudu maso gabas na gama, Atiku
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya nuna karfin gwiwar cewa zai lallasa Peter Obi da Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.
Atiku wanda ya ce shi ya fi cancanta ya gaje Buhari a zabe mai zuwa ya ce yankin kudu maso gabas nashi ne.
Asali: Legit.ng