2023: Sauya Shekar Inuwa Ba Zai Ragi APC da Komai Ba, Gwamna Masari

2023: Sauya Shekar Inuwa Ba Zai Ragi APC da Komai Ba, Gwamna Masari

  • Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina yace sauya shekar Mustapha Inuwa zuwa PDP ba zata jawo wa APC cikas ba a 2023
  • Mustapha Inuwa, tsohon Sakataren gwamnatin Masari, ya bar APC ne bayan shan ƙasa a zaben fidda gwani hannun Radda
  • Ana ganin tsohon SSG na daga cikin ƙusoshin mulkin APC, sai dai Masari yace ba zai iya taɓuka komai ba

Katsina- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa sauya sheƙar da tsohon sakataren gwamnatin jihar da ya gabata, Mustapha Inuwa, ya yi zuwa jam'iyyar PDP, ba zai kawo wa jam'iyyar APC cikas ba a 2023.

Gwamnan yayi bayanin cewa daga cikin jagororin jam'iyyar 324 na ƙaramar hukumar Danmusa, inda Mustapha Inuwa ya fito, 26 ne kacal suka sauya sheƙa tare da shi zuwa jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Tana Neman Karewa Atiku, Wasu Gwamnonin PDP Sun Fara Shirin Komawa Bayan Tinubu a 2023

Gwamna Aminu Bello Masari.
2023: Sauya Shekar Inuwa Ba Zai Ragi APC da Komai Ba, Gwamna Masari Hoto: Aminu Bello Masari/facebook
Asali: Facebook

Gwamnan ya ƙara da cewa da shi da sauran ƴaƴan jam'iyyar APC kwata-kwata ba su damu da sauya sheƙar da ya yi ba, kamar yadda This Day ta rahoto.

Masari, ya nuna ƙwarin guiwar sa kan cewa jam'iyyar APC zata lashe zaɓukan, inda ya haƙiƙance cewa masu sauya sheƙar sun shiga ɗimuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Inuwa, wanda ya tsaya takarar gwamna a zaɓen fidda gwanin APC, ya sha kaye a hannun Dr. Umar Dikko Radda, ya fice daga jam'iyyar shi da ƙungiyoyin dake mara masa baya har 627 a cikin mazaɓu 361 na jihar zuwa jam'iyyar PDP.

“Mu na son sanin da shi da waye suka fice saboda a ƙaramar hukumar sa ta Danmusa, muna da jagororin jam'iyya 324, guda 26 ne kacal suka tafi tare da shi.
“Gaba ɗaya shugabannin APC a ƙaramar hukumar sa suna nan sannan dukkanin wasu masu ruwa da tsaki a yankinsa ba su bishi ba.

Kara karanta wannan

"Ku Taimaka Ku Zabi APC Sak a 2023" Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Roki 'Yan Najeriya

"Yau, wani zai gaya maka cewa ya yarda da Allah sannan zai iya ƙara maka da cewa abu indai rabon sa ne ba zai taɓa ƙetare sa ba. Zai kuma ce duk wani abu na cigaba ga jihar ko ga ƙasar zai bi."

A cewar Masari duk wannan zancen daɗin baki ne, inda ya kara da cewa:

"Duk muna faɗin hakan, amma da zarar ya faru, bamu samu abinda muke so ba, sai mu fara ɗagawa mutane yatsa cewa sune suka ja mana bamu samu ba. Ina Allah ɗin da kake kira?"
Cikin sa'a, muna da ƴan takara tara waɗanda suka fafata a zaɓen fidda gwanin, takwas daga ciki harda wanda ya samu har yanzu suna tare da mu sannan sauran ɗayan ya fice saboda wasu dalilai na ƙashin kansa."
"A lokacin da wani zai fice sannan wani yake shigowa. Saboda haka ko ƙadan ba mu damu ba."

Duk labarin da ake yaɗawa kan Inuwa ba gaskiya bane

Kara karanta wannan

2023: Insha Allahu 'Yan Najeriya Ba Zasu Yi Dana Sani Ba Idan Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu

Legit.ng ta tuntubi wani jigon APC a yankin karamar hukumar Ɗanja, jihar Katsina, Usman Gide, da ake kira Bandiro, ya faɗa wa wakilinmu cewa tabbas fitar tsohon SSG ba ta taba damar jam'iyyar ba.

Bandiro, tsohon ɗan takarar Kansila a gundumar Dabai, yace da farko sun ɗan ji ba daɗi da fitar Inuwa ganin yadda aka ce ya tafi da ƙusoshi amma da suka bincika sai suka gano duk ƙarya ce.

Jigon yace:

"Mustapha Inuwa babban jigon siyasa ne amma ya ɓata rawarsa da tsalle, mutanen dake tare da shi kansu basu yarda sun bi shi PDP ba. Kamar yadda gwamna ya faɗa shi kaɗai ya tafi."
"Kuma abun takaicin duk wata hanyar rarrashinsa bayan zaɓen fidda gwani an bi, amma ya ƙeƙashe kasa. Labarin da ake yaɗawa ya tafi mutane da kungiyoyi duk karya ne."

"Ƙa Ci Zabe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Mutane Suka Tarbi Tinubu a Neja

Kara karanta wannan

2023: Daraktan Yakin Neman Zaben Atiku Ya Gana da Gwamnan Tsagin Wike, Bayanai Sun Fito

A wani labarin kuma Bola Tinubu Ya gaza magana sakamakon yadda mutane suka cika maƙil suna faɗin 'Kaci zabe ka ci zabe,' a gangamin Neja

Dubun dubatar mutane ne suka tarbi Bola Tinubu yayin da tawagarsa ta shiga filin gangamin kamfen a jihar Neja, 'kaci zabe ba sai ka yi magana,' ne ke tashi a iska daga bakunan mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262