Hamza Al-Mustapha da Wasu ‘Yan Takara da Ya Kamata a Lura da Su da Kyau a 2023

Hamza Al-Mustapha da Wasu ‘Yan Takara da Ya Kamata a Lura da Su da Kyau a 2023

  • A watan Fubrairun shekarar 2023, mutanen Najeriya za su zabi wanda zai zama sabon shugaban kasa
  • Akwai ‘yan siyasa 18 da suka nuna su na sha’awar cin gadon kujerar Muhammadu Buhari a Aso Rock
  • Akwai ‘yan takaran da ake ganin ba za su je ko ina ba, amma hasashe na nuna za su iya bada mamaki

FCT, Abuja – A yayin da ‘yan Najeriya suke shiryawa babban zabe a farkon 2023, an fi maida hankali a kan ‘yan takara hudu a zaben shugaban kasa.

‘Yan takaran da ake gani su ne a gaba su ne Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar da ke PDP, ‘Dan takaran LP, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a NNPP.

A rahoton nan na Legit.ng za a ji akwai wasu ‘yan takara biyar da za a gwabza da su a filin zabe:

Kara karanta wannan

2023: Babu wani Tinubu ko Atiku, ni zan lashe zaben 2023, Kwankwaso ya hango wani haske

1. Kolawole Abiola (Peoples Redemption Party, PRP)

Tun a zaben tsaida gwanin PRP, Kolawole Abiola ya nuna shi ba karamin ‘dan siyasa ba ne, ya gaji abin a jininsa daga mahaifinsa, Marigayi MKO Abiola.

Abiola ya doke Dr. Usman Bugaje wajen samun tikitin shugaban kasa a PRP. Bugaje tsohon ‘dan majalisar tarayya, kuma ya taba aiki da Atiku Abubakar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Adewole Adebayo (Social Democratic Party, SDP)

Daga cikin abin da Adewole Adebayo yake takama da shi a zabe mai zuwa shi ne, su ne masu mafi karancin shekaru a masu neman kujerar shugabancin kasar.

Jam’iyyarsa ta SDP tana da ofisoshi a fadin Najeriya, kuma kwararren Lauya ne wanda ke da lasisin aiki a kasashen Australiya, Kanada, Birtaniya da Amurka.

Hamza Al-Mustapha
Hamza Al-Mustapha da Immumole Christopher Hoto: AA, AP
Asali: Facebook

3. Imumolen Christopher (Accord Party, AP)

Mafi yawan mutane su na raina Imumolen Christopher a zaben shekara mai zuwa, amma akwai yiwuwar matashin Farfesan ya bada mamaki a wasu wurare.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Irin Na Tinubu, Ya Tafka Katuwar Katobara Gaban Jama’a Wajen Kamfe

Baya ga Joint Professional Training and Support International Limited da ya bude, ‘dan takaran na jam’iyyar AP yana da mabiyan da ba za a rasa a Najeriya ba.

4. Omoyele Sowore (African Action Congress, AAC)

Ba wannan karo Omoyele Sowore ya fara yakin neman zabe ba, daga 2019 zuwa yanzu, ana sa ran ya kara samun kwarewa da gogewa a kan siyasar kasa.

‘Dan jaridar ya yi suna wajen kare hakkin Bil Adama, baya ga haka jam’iyyar AAC da ya kafa tayi suna a Najeriya, tana da ‘yan takara da-dama a zaben badi.

5. Hamza Al-Mustapha (Action Alliance, AA)

‘Dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar AA, tsohon Manjo ne a gidan Soja. Hamza Al-Mustapha ne dogarin Janar Sani Abacha a lokacinsa.

Ana ganin Manjo Al-Mustapha ya san sirrin Najeriya, kuma yana da kwarewa da ilmin da zai shawo kan matsalar rashin tsaro da rashin ayyukan yi a kasa.

Tallafin man fetur sai ya tafi

Kara karanta wannan

Shugaba a PDP ya Fallasa Tinubu, Kuma Yana barazanar ba Zai Zabi Atiku a 2023 ba

Idan har ana so Najeriya ta cigaba, an rahoto Malam Nasir El-Rufai yana cewa sai gwamnatin tarayya ta hakura da biyan tallafin man fetur a shekarar badi.

Amma Nasir El-Rufai yana ganin idan wanda ya zama shugaban kasa ya cire tallafin, ba dole ba ne mutane su sake zaben shi a 2027 saboda zai yi bakin jini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng