2023: Atiku Abubakar Ya Shirya Zama da Gwamnan Wata Jam'iyya Da Sarakunan Jiharsa
- Mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, zai gana da gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo
- A wata sanarwa da kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa ya fitar, yace Atiku zai ziyarci Anambra kamfe ranar Alhamis
- PDP tace fa kafa kwamiti na musamman da zai shiga tsakani don kawo karshen rigimar tsagin G5
Anambra - Jam'iyyar PDP tace shiri ya yi nisa na karban ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, a jihar Anambra ranar Alhamis domin gangamin yakin neman zaɓe.
Punch tace Daraktan kamfen Atiku/Okowa na jihar Anambra, Dakta Obiora Okonkwo ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai ranar Laraba a Awka.
Yace wannan gangamin kaddamar da yakin neman zaben PDP da zai guda a Awka gobe zai tabbatar wa duniya cewa Anambra ta PDP ce.
Okonkwo yace jirgin Atiku da tawagarsa na dira a Awka zai wuce zuwa gidan gwamnati domin ziyartar gwamnan Anambra, Farfeda Charles Soludo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yace bayan gana wa da mai girma gwamna, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP zai kuma tattauna da Sarakunan Gargajiya karƙashin shugaban majalisar Sarakunan kudu maso gabas, Obi Alfred Nnaemeka Achebe, Sarkin Onitsha.
PDP ta shirya tawaga ta musamman don kawo karshen rikicin G5
Game da rigingimun PDP, Mista Okonkwo yace tuni aka haɗa tawaga ta musamman kuma sun fara aiki ba kama hannun yaro domin kawo karshen kace nace tsakanin ɗan takara da tawagar G5.
Yace har yanzun ana ci gaba kokarin haɗa Atiku da mambobin G5 a inuwa ɗaya kuma jihar Anambra ta shirya tsaf don tabbatar da nasarar Atiku a zaɓen 2023.
A cewarsa, bayan haka, "Ɗan takarar shugaban kasa zai kaddamar da Ofishin Kamfen PDP a mahaɗar Kwata cikin birnin Awka, daga nan zai wuce ɗakin taro ya gana da masu ruwa da tsaki."
PDP Ta Ɗau Zafi, Wike Da Wani Gwamnan Arewa Sun Yi Watsi da Atiku Yayin da Suka Ci Karo a Filin Jirgi
Bugu da kari yayin wannan ziyara da Atiku zai kawo jihar Anambra ne zai kaddamar fara yakin neman zaben shugaban kasa a Alex Ekwueme Square.
A wani labarin kuma Jerin Jihohin Arewa da PDP Ba Ta Taɓa Samun Nasarar Zabe Ba Tun 1999 Da Abinda Zai Faru a 2023
A 1999 da mulkin demokaradiyya ya dawo Najeriya, jam'iyyar PDP ce ta mamaye mafi yawan jihohin Najeriya da kujerar shugaban kasa.
Tarihi ya nuna cewa zuwa shekarar 2007 PDP ta kafa gwamnati a jihohi 31 cikin 36, amma akwai wasu jihohin arewa guda biyu da suka gagari PDP har zuwa yau.
Asali: Legit.ng