Gumi ga ‘Yan Najeriya: Katin Zabe Yafi Kowanne Satifiket, Yafi Fasfotin Fita Ketare

Gumi ga ‘Yan Najeriya: Katin Zabe Yafi Kowanne Satifiket, Yafi Fasfotin Fita Ketare

  • Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, malamin addinin Islama mazaunin jihar Kaduna ya bayyana cewa ya karba katin zabensa
  • Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su garzaya domin karbo nasu saboda yafi duk wani satifiket ko fasfotin fita ketare muhimmanci
  • Gumi yace wannan ne makamin da za a tabbatar da samun shugabanci nagari kuma yana da tabbacin cewa kuri’u zasu yi amfani a zaben 2023

Kaduna - Fitaccen malamin addinin Islama mazaunin jihar Kaduna, Sheikha Ahmad Abubakar Gumi a ranar Laraba ya bayyana cewa katin zabe yafi amfani kan dukkan satifiket din makaranta da fasfotin fita ketare.

Sheikh Gumi
Gumi ga ‘Yan Najeriya: Katin Zabe Yafi Kowanne Satifiket, Yafi Fasfotin Fita Ketare. Hoto daga Sheikh Ahmed Gumi
Asali: Facebook

Yayi kira ga jama’a da su karba katikan zabensu na dindindin kuma su fita su yi zaben 2023 don Samun shugabanni nagari.

Gumi, wanda yace kuri’u zasu yi aiki a zaben 2023, ya bayyana cewa samun katin zabe ne hanya daya da za a yi zabe inda ya ja kunnen ‘yan Najeriya kan cewa dole ne su yi zabe gudun a kwace musu ‘yancinsu kuma a arce da shi.

Malamin yayi wannan kiran bayan ya karba katin zabensa na dindindin kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook inda yayi kira ga ‘yan Najeriya da su sauke hakkinsu ba tare da an tirsasa musu ba, tsoro ko barazana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A rubutun da yayi:

“Ku zabi zabinku ba tare da tirsasawa, tsoro ko bata suna ba.
“Kuri’unku zasu yi amfani don haka ku samu katikan zaben ku saboda ita ce hanya daya da za ku karba iko ko kuma ku kwace mulki ku yi gaba da shi.
“Katin zaben ka. Godiya ta tabbata ga Allah, na samu nawa. Don Allah garzaya ka samu naka. Ba tare da kurantawa ba, yafi dukkan takardun da mutum ke dasu, yafi fasfotin fita ketare ko duk wasu satifiket.
“Wannan kati ne dake karfafa ka wurin zabar shugaba kuma ba a bukatar a zaunar da kai kan bayanin muhimmancin shugabanci.”

INEC ta fitar da ranar fara karbar katin zabe

A wani labari na daban, hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, ta sanar da cewa ranar 12 ga watan Disamba zata fara raba katikan zabe na dindindin.

Kamar yadda hukumar ta bayyana, za a raba katikan a kananan hukumomi 774 na fadin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel