Hukumar Zabe ta INEC ta Sanar da Ranar Fara Karban Katikan Zabe

Hukumar Zabe ta INEC ta Sanar da Ranar Fara Karban Katikan Zabe

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta saka ranar 12 ga watan Disamban matsayin ranar fara karbar katikan zabe na dindindin
  • Kamar yadda hukumar ta bayyana, za a kare karbar katikan zaben a ranar 22 ga watan Janairun 2023 a sabuwar shekara
  • Za a bude dukkan ofisoshin a dukkan kananan hukumomi 774 na fadin kasar nan har ranakun Asabar da Lahadi

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, a ranar Juma’a ta sanar da cewa ‘yan kasa da suka yi rijistar katin zabe kafin zuwan zaben 2023 zasu fara karba katin zabensu na dindindin daga ranar 12 ga watan Disamban 2022.

Katikan zabe
Hukumar Zabe ta INEC ta Sanar da Ranar Fara Karban Katikan Zabe. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Wannan na kunshe ne a takardar da aka bai wa manema labarai a Abuja.

Kamar yadda takardar tace, hukumar tayi taro a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamban 2022 kuma suka tattauna kan wasu muhimman abubuwa da suka hada da da da fara karbar katikan zabe a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

Jaridar Punch ta rahoto tun farko cewa, hukumar tayi taro a Legas da kwamishinonin zabe na jihohi 36 na fadin kasar nan daga 28 na watan Nuwamba zuwa 2 ga Disamban 2022.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A taron, hukumar ta kammala dukkan tsari tare da fitar da jadawalin karbar katikan zabe.

Kamar yadda jaridar Channels ta rahoto, takardar wacce ta samu da hannun kwamishinan ilimantar da masu kada kuri’a, Festus Okoye, tace:

“Hukumar ta saka Litinin, 12 ga watan Disamban 2022 zuwa ranar Lahadi, 22 ga watan Janairun 2023 a dukkan kananan hukumomi 774 na kasar nan.
“Hukumar ta yanke hukuncin bude wuraren rijistar zabe 8,809 na kananan hukumomin daga Juma’a 6 ga watan zuwa Lahadi, 15 ga watan Janairun 2022.
“Wadanda basu samu damar karbar katikan zabe su ba a kananan hukumomin zasu iya wurin rijistarsu su karba.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tura Shugaban Jam'iyyar APC Gidan Gyaran Hali Kan Laifi Daya

“Bayan ranar 15 ga Janairun 2023, za a mayar da su ofisoshin hukumar zabe ta kowacce karamar hukuma har zuwa ranar 22 ga watan Janairun 2023.
“Jama’a zasu iya karbar katikan zabensu daga karfe 9 na safe zuwa karfe 3 na yammacin kowacce ranar har da ranakun Asabar da Lahadi.”

Yan daba sun Kona ofishin INEC a Ebonyi

A wani labari na daban, wasu miyagun ‘yan daba sun kai farmaki ofishin hukumar zabe mai zaman kanta a karamar hukumar Izzi ta jihar Ebonyi.

An gano cewa, miyagun sun kai farmakin inda suka kone katikan zaben jama’a tare da wasu kayayyaki masu amfani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel