Ni Zan Lashe Zaben 2023; APC da PDP Sun Mutu, Kwankwaso Ya Fada Ma ’Yan Najeriya
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yana da kwarin gwiwar casa abokan hamayyarsa a zaben 2023 mai zuwa nan da badi
- Dan takarar a jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari ya ce shi zai gaji Buhari ba tare da wata matsala a zabe mai zuwa
- Ya bayyana hakan ne a jihar Ekiti yayin da yake fadada karbuwarsa a aniyarsa ta zama shugaban kasan Najeriya a yankin Kudu maso Yamma
Ekiti, Ado-Ekiti – Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, ya hango kansa a matsayin shugaban kasan Najeriya a zaben 2023.
Ya bayyana cewa, ya yi has ashen akwai haske game da nasararsa a zaben mai zuwa duba da yadda ya samu karbuwa a idon ‘yan kasar nan, Vanguard ta ruwaito.
Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne ya fadi wannan batu ne a jihar Ekiti lokacin da yake jawabi a fadar mai martaba Ewi na Ado-Ekiti, Oba Rufus Adeyemo Adejugbe, wanda ya karbi bakuncin NNPP.
Da yake magana a masarautar, Kwankwaso ya tuna yadda gwamnatin APC ta kafu a 2015 da kuma yadda ta ba ‘yan Najeriya kunya ta hanyar gaza tabuka abin kirki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce:
“Idan za a yi zabe yau, NNPP na hango haske, babu wata jam’iyyar siyasa da za ta lallasa NNPP, PDP ta samu lahani a yankin Kudu maso Gabas saboda samun wasu jam’iyyun siyasa, kuma tabbas a Arewa, mun mamaye PDP, ko da a Kudu maso Kudu, basu da wani tasiri saboda hamayyar zaben fidda gwani da aka yi.
“Ita kuwa APC, ta gaza a idon ‘yan kasa, babu dan Najeriya mai tunani da so a ci gaba a yadda ake, ma’ana wannan mummunan yanayi ya ci gaba.”
2023: Kwankwaso ya fadi daidai da za su sa ‘yan Najeriya su zabe shi
Kamar yadda yazo a rahoton Daily Independent, Kwankwaso ya ce ya yi ayyuka masu tasiri da ciyar da jihar Kano gaba lokacin da ya rike kujerar gwamna.
Kwankwaso ya ce zai yi irin abin da ya yi a Kano idan aka bashi dama ya gaji Buhari a zaben 2023 na badi.
Ya kara da cewa:
“APC da PDP sun mutu, sun gama yawo, kuma jam’iyyarmu ce za ta ci zaben nan na badi na shugaban kasa da yardar Allah, mun yi karfi a Arewa, kuma tabbas za mu ci zabe.”
Kwankwaso dai zai fafata da manyan jiga-jigan siyasan Najeriya a jam’iyyun siyasa mafi karbuwa da shahara a Najeriya, Kudu da Arewa.
‘Yan takarar da Kwankwaso zai gwabza dasu sun hada da; Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na jam’iyyar Labour da dai sauran ‘yan takara a sauran jam’iyyu.
Jam'iyyar PDP kuwa na kara shiga damuwa, jiga-jiganta sun ce ba za su zabi Atiku ba har sai ya cika wasu ka'idoji da suke so.
Asali: Legit.ng