Sanatoci Sun Dauko Aiki, Za a Ragewa Shugaban Kasa Iko Kan Nadin Shugaban EFCC
- Majalisar dattawa ta yi muhawara a kan kudirin da zai haramtawa shugaban kasa tsige shugaban hukumar EFCC
- Idan kudirin ya samu shiga, shugaban kasa zai rasa damar tsige shugaba a EFCC ba tare da amincewar Sanatoci ba
- Sanatan yankin Arewacin jihar Enugu, Chukwuka Utazi ya gabatar da kudirin, kuma yana ta samun karbuwa
Abuja - Kudirin da zai hana shugaban kasa tunbuke shugaban hukumar EFCC a Najeriya, ya tsallake matakin muhawara na biyu a majalisar dattawa.
A ranar Talata, 13 ga watan Disamba 2022, Premium Times ta ce an tattauna a kan wannan kudiri wanda zai rake karfin da doka ta ba shugaban Najeriya.
Kudirin yana kokarin canza dokar da ta kafa EFCC ta yadda dole a bukaci amincewar 'yan majalisar dattawa kafin shugaban kasa ya tsige shugaban hukumar.
Sanata Chukwuka Utazi ya ce ya kawo kudirin domin daina wasa da wa’adin shugabannin EFCC. Abin da ya rage shi ne a tattauna a kai gaban kwamiti.
Idan Chukwuka Utazi ya yi nasara, nan gaba dole sai shugaban kasa ya samu rinjayen ‘yan majalisar dattawa kafin ya nada ko ya cire shugaba a EFCC.
Sanatan na Enugu ta Arewa yake cewa majalisar tarayya tayi kokari wajen ganin an hana shugaban kasa cire shugabannin hukumomin ICPC da NFIU kai-tsaye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin ba haka yake a dokar EFCC ba, wannan ya sa mai tsawatar da marasa rinjaye a majalisar yake ganin za iyi kyau hukumar tayi koyi da sauran takwarorinta.
Za a hana dauko Shugaban EFCC a waje
Wata kwaskwarima da Sanatan yake so ayi ita ce a takaita shugabancin EFCC ga jami’in hukumar, ta yadda ba zai halatta a dauko shugaba daga waje ba.
A jawabinsa, ‘dan majalisar ya yabi Mai girma Muhammadu Buhari da wannan karo ya dauko ‘dan cikin gida (Abdulrasheed Bawa), ya rike masa hukumar.
Rahoton ya ce Sanatocin da suka tashi tofa albarkacin bakinsu, sun goyi bayan Utazi.
Sanata George Sekibo na gabashin Ribas yace garambawul din zai kawo gyara, wannan shi ne ra’ayin James Manager mai wakiltar kudancin jihar Delta.
Sam Egwu ya yabi Bawa, yace amma ba dole ba ne wanda zai gaje shi ya zama irinsa, don haka ba ya goyon bayan a ce dole daga hukumar za a samu shugaba.
Garba Shehu ya yi Kazaure raddi
An samu labari Malam Garba Shehu ya yi cikakken bayani kan tarihin nada kwamitin Muhammadu Gudaji Kazaure domin ya binciko satar kudi a CBN.
Hon. Kazaure ya ce N89tr ake zargin sun yi kafa, amma Hadimin shugaban kasar ya ce duka dukiyar da ke bankuna ba su kai rabin abin da Kazaure yake kira ba.
Asali: Legit.ng