Zaben 2023: Atiku Ya Dauki Alkawarin Dawo Da Zaman Lafiya Jihar Filato

Zaben 2023: Atiku Ya Dauki Alkawarin Dawo Da Zaman Lafiya Jihar Filato

  • PDP ta kaddamar da yakin neman zabenta a garin Jos, babban birnin jihar Filato a ranar Talata, 13 ga watan Disamba
  • Atiku Abubakar ya sha alwashin dawo da zaman lafiya da habbaka tattalin arziki yayin da yake jawabi ga al’ummar Filato
  • Kamar yadda aka sani jihar Filato na fama da rikicin addini, kabilanci da na makiyaya da manoma

Plateau - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya ba mazauna Fialto tabbacin dawo da zaman lafiya da habbaka tattalin arziki idan aka zabe shi.

Atiku ya yi alkawarin ne yayin da yake jawabi ga mabiya jam'iyyar a yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP a filin wasa na Rwang Pam da ke Jos a ranar Talata, 13 ga watan Disamba, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan PDP Sun Shiga Zulumi, An yi Taron Gangamin Kamfen, Fili a Bushe a Wata Jahar Arewa

Atiku a Jos
Zaben 2023: Atiku Ya Dauki Alkawarin Dawo Da Zaman Lafiya Jihar Filato Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Atiku ya ce:

"Yanzu, mutanen jihar Filato, tamkar na dawo gida ne a yau. Dawowa gida ne saboda na zauna a jihar nan tsawon fiye da shekaru 28. Mun yi alkawarin cewa za mu dawo da zaman lafiua a wannan jaha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za mu kuma dawo tare da farfado tattalin arzikin jihar nan."

Zan gyara hanyoyin da ke sada Filato da sauran jihohi, Atiku

Atiku ya kuma bayar da tabba,cin cewa za a mayar da hankali wajen gyara hanyoyin a jihar kasancewar yankin na sada mutum da sauran yankunan kasar, rahoton Channels TV.

"Za kuma mu tabbatar da ganin cewa jihar nan ta sadu da jihohi masu makwabtaka. APC ta yi watsi da duk hanyoyjn da ke aada Filato da sauran jihohi a kasar. Mun yi alkawari saboda ku jahar PDP ce."

Gangamin ya samu halartan jami'ai da jiga-jigan jam'iyyar ciki harea abikin takarar Atiku, Ifeanyi Okowa, shuvaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu; darakta janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Aminu Tambuwal da mambobin jiha da na majalisar dokoki na kasa da sauransu.

Kara karanta wannan

PDP Ta Ɗau Zafi, Wike Da Wani Gwamnan Arewa Sun Yi Watsi da Atiku Yayin da Suka Ci Karo a Filin Jirgi

Da farko tawagar yakin neman zaben shugaban kasar aun ziyarci Gbong Gwom Jos Da Jacob Gyang Buba a fadarsa da babban limamin Anglican na Jos, Rabaran Benjamin Kwashu da Sheikh Yahaya Jebgri.

Mutane basu hallara ba sosai a gangamin yakin neman zaben Atiku a Filato

A wani labarin, mun ji cewa filin wasa da aka gudanar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP bai cika da jama'a ba.

Sabanin yadda wajen ya cika babu masaka tsinke a lokacin yakin neman zaben Bola Tinubu na APC, jama'a basu yi tururuwa ba a na Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng