Sanatan PDP Ya Ba Buhari Uzuri, Ya Fadi Inda Aka Samu Matsala a Gwamnatin APC
- Danjuma La’ah yana ganin Muhammadu Buhari ya samu matsala ne daga wadanda ke zagaye da shi
- Sanatan na PDP ya ce wadanda aka ba mukamai ba suyi abin da ya kamata, kuma ba a duba aikinsu
- La’ah ya bayyana abin da ya hana shi komawa APC duk da jam’iyyar ta mamaye yankin da ya fito
Abuja – Sanata Danjuma La’ah ya yi hira da jaridar Punch a kan zamansa a majalisar dattawa, siyasar Najeriya da kuma salon gwamnatin APC mai-ci.
Danjuma La’ah ne shugaban marasa rinjaye a majalisa, shi kadai ne Sanatan jam’iyyar PDP daga yankin Muhammadu Buhari na Arewa maso yamma.
Sanatan yake cewa duk da jam’iyyar APC tayi karfi a shiyyarsa, bai sauya sheka daga PDP ba.
“Ban ga dalilin sauya-sheka ba. Zan iya tunawa shugaban kasa da kan shi ya tambaye ni meyasa ba zan shiga APC ba, na fada masa ina kare martabar PDP ne.”
Akwai kuskuren da ‘yan Najeriya ke yi a halin da ake ciki. Dole mutum ya yi hattara da kashe-kashen da ake yi, idan mutum yana adawa, babu mai goyon bayansa."
- Danjuma La’ah
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
La'ah v Nasir El-Rufai
Sanatan adawan ya zargi Gwamna Nasir El-Rufai da yin bakin kokarinsa na ganin ya hana shi zuwa majalisar dattawa, amma bai yi nasara a kansa ba.
La’ah yake cewa saboda Nasir El-Rufai yana Gwamna, babu yadda ya iya da abin da ake yi a majalisa, musamman idan Sanata yana yi wa jama’ansa aiki.
Har ila yau, Sanatan na Kudancin Kaduna ya zargi wasu Gwamnonin da yin watsi da wasu bangarorin jihohinsu musamman wadanda ba su zabe su ba.
Rikicin gidan PDP
A game da rikicin PDP, ‘dan siyasar bai ganin cewa lamarin zai kawo masu cikas a zabe mai zuwa, yace burinsu shi ne yadda za a kai Atiku/Okowa ga nasara.
An rahoto shi yana cewa Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa sun yi bakin kokarinsu wajen tallata manufofinsu, amma duk da haka wasu ba za su zabe su ba.
Gwamnatin Buhari
Da aka yi masa tambaya a kan mulkin Buhari, La’ah ya ce a ra’ayinsa shugaban kasar yana da niyya mai kyau, amma bai yi dace da mukarabbai a mulkinsa ba.
A cewarsa ba a duba aikin da wadanda aka ba mukamai suke yi, kuma ba a yin kokari wajen ganin an tabbatar wadanda aka nada, sun yi abin da ake bukata.
A cikin 100%, ‘dan majalisar na Kudancin Kaduna ya ce zai ba gwamnatin Buhari 50% zuwa 60%.
Siyasar 2023
Kun samu rahoto a Gwamnonin Arewa maso yamma da ke barin mulki, Aminu Tambuwal da Atiku Bagudu ne kurum za su shiga takarar Majalisar Dattawa.
Nasir El-Rufai, Abdullahi Ganduje, Badaru Abubakar da Aminu Masari ba su cikin ‘Yan takara a 2023, shi kuma Bello Matawalle ne zai nemi tazarcen Gwamna.
Asali: Legit.ng