Insha Allahu 'Yan Najeriya Ba Zasu Yi Dana Sani Ba Idan Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu
- Ɗan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu, yace da ikon Allah mutane ba zasu yi dana sani ba idan suka zabe shi a 2023
- Tsohon gwamnan Legas din ya sha alwashin kawo karshen ayyukan ta'addancin 'yan binidga a arewacin Najeriya
- A yau Talata jam'iyyar APC mai mulki ta kaddamar da yakin neman zaɓen shugaban ƙasa a arewa ta yamma
Kaduna - Mai neman zama shugaban kasa a inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace da ikon Allah 'yan Najeriya ba zasu yi dana sani ba idan suka zaɓe shi a 2023.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Tinubu ya ba da wannan tabbacin ne a wurin gangamin yakin neman zaɓensa dake gudana a Kaduna ranar Talata.
Gamgamin Kaduna somin taɓi ne na fara yakin neman zaben shugaban kasa na APC a shiyya mafi yawan kuri'u a Najeriya watau arewa maso yamma.
2023: "Ka Ci Zaɓe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Magoya Baya Suka Yi Maraba da Tinubu a Jihar Arewa
Da isarsa Kaduna ranar Litinin, Bola Tinubu ya zarce zuwa Birnin Gwari, ƙaramar hukumar da ta'addancin 'yan bindiga ya fi addaba a jihar, kamar yadda Dailypost ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Alkawurran da Tinubu ya ɗauka a Kaduna
Da yake jawabi ga dandazon mutanen da suka fito tarbansa, tsohon gwamnan jihar Ƙegas din yace idan aka zaɓe shi a 2023, zai kawar da 'yan bindigan daji daga doron duniya.
Haka zalika ya ɗauki alƙawarin fifita hanyoyin rage zaman kashe wando, samar da aiki mai gwabi ga matasa da kuma haɓaka noma ta hanyar kafa hukumar kasuwanci.
A jawabinsa, Tinubu ya ce:
"Muna godiya ga Allah SWT da ya kawo ku nan kuma muna gode muku da kuka ci gaba da goyon bayan jam'iyyar mu, ba zaku yi dana sani ba insha Allahu."
Yan Najeriya Sun Samu Sabon Sumfurin Shugaba Buhari, Doguwa Ya Jaddada Wanda Ya Dace da Mulki a 2023
"Duk waɗan nan masu ta da ƙayar baya, masu garkuwa, masu kashe-kashe da suka hana Kaduna zaman lafiya da arewacin Najeriya ina tabbatar muku zamu kawar da su Insha Allah."
"El-Rufai ya zuba maku aiki, ku kewaye Kaduna zaku ga yadda ta tsaru amma duk shugaban da bai samu magaji nagari ba bai cika nagartaccen shugaba ba. Ya baku matashi, Uba Sani ya zama gwamnan ku na gaba."
Legit.ng ta zanta da wani mamban APC kuma ɗan amutun Bola Tinubu a karamar hukumar Kaduna ta kudu, Zaharadden Aliyu, yace ai Jagaba ya gama magana tunda ya sa Allah.
Aliyu, wanda ya halarci gangamin APC a Filin Ahmadu Bello, yace wannan taron ya nuna har yanzun ruwa na magajin datti, mutane na nan tare da jam'iyyar APC.
A cewarsa, "An ce aiki ke tabbatar da furuci, kowa ya gani da zuwan Tinubu ya zarce Birnin Gwari inda matsalar yan bindiga ta yi wa katutu, lokacin da zai dawo yamma tayi liƙis, shin kunsan wane lokaci ya fi hatsari a hanyar nan?"
"Wannan kaɗai ya isa ya tabbatar wa yan Najeriya da maganarsa ta cewa zai murkushe yan iskan nan da zaran ya zama shugaban kasa, muna tare da shi, al'ummar Kaduna na tare da shi."
Ɗan siyasan ya shaida wa wakilinmu cewa duk wanda ya halarci gangamin APC ko dai ya ƙara tabbatar da akwai alamun nasara ko kuma hankalinshi ya tashi idan ɗan adawa ne.
Ba Abinda Zai Hana Bola Tinubu Zama Shugaban Kasa a 2023, Babban Fasto
A wani labarin kuma Wani Babban Malami a Jihar Legas ya yi hasashen cewa ba mai iya dakatar da Tinubu daga zama shugaban kasa a 2023
Malamim Cocin mai suna, Fasto Adamu David Tunji, yace duk da sukar da ɗan takarar APC ke sha daga wasu sassan ƙasa, hakan ba zai hana shi nasara ba.
Ya kuma shawarci 'yan uwansa Malaman Coci da kunguyar CAN su daina gurɓata tunanin mabiyansu da zancen takarar Musulmi da Musulmi.
Asali: Legit.ng