Sanata Abdullahi Adamu: Tinubu Ne Magajin Shugaban Buhari

Sanata Abdullahi Adamu: Tinubu Ne Magajin Shugaban Buhari

  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana Bola Ahmed Tinubu matsayin magajin Buhari
  • Ya sanar da hakan ne a garin Kaduna yayin gangamin ralin jam'iyyar da take yi a yankin arewa maso yammacin Najeriya
  • Ya bayyana cewa, ganin irin gagarumin taron da suka hada kadai na nuna nasara karara kuma zasu lashe zaben 2023 mai zuwa

Kaduna - Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa ya bayyana cewa ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne magajin Buhari.

Ya bayyana hakan ne a yayin ralin gangamin yakin neman zaben APC na arewa maso yamma a Kaduna ranar Talata, Daily Trust ta rahoto.

Tinubu a Kaduna
Sanata Abdullahi Adamu: Tinubu Ne Magajin Shugaban Buhari. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Adamu ya bayyana dalilinsa

Sanata Adamu yace yawan jama’ar da suka halarcin ralin kadai yana nuna sunan da jam’iyyar tayi.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tinubu, Ganduje, El-Rufai na can a Kaduna don kaddamar da kamfen APC a Arewa maso Yama

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bari in gabatar muku da shugaban kasanmu na gaba, wanda zai gaji shugaban kasa Buhari, gareku, Bola Ahmed Tinubu.
“Nan da 25 ga watan Fabrairun 2023, ku fito kwan ku da kwarkwata ku zabi Tinubu da dukkan ‘yan takarar jam’iyyar APC.”

- Yace.

Ya kara da mika godiya ga masoyan jam’iyyar na Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Sokoto da Kaduna kan yadda suka fito suka halarci ralin.

Gwamna El-Rufai yayi jawabi

A jawabin Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, yace APC ya ce tasa wannan gagarumin taron ya hadu yayin da yake mika godiya ga duk wadanda suka fito ballantana mata da matasa.

A ranar Litinin ne Tinubu ya sha alwashin ganin bayan ta’addanci da kashe-kashe idan aka zabe shi shugaban kasa.

Ya sanar da hakan yayin da ya kai ziyara ga Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Jibril Mai Gwari.

Kara karanta wannan

Ta karewa Tinubu a Arewa, Atiku ya karbi mambobin APC 10,000 zuwa APC a jihar Arewa

Ya kara da shan alwashin yi wa jama’a hanyoyin samun ruwa domin magance matsalolin rashin ruwa inda yace zai tabbatar da Najeriya ta gyaru ko da kuwa hakan zai masa wahala.

Ya bada tallafin N50 miliyan ga wadanda ta’addancin ‘yan bindiga ya ritsa dasu a karamar hukumar.

“Zamu samar muku da zaman lafiya, ga wadanda lamurran ta’addanci ya shafa, Allah ya gafarta musu.
“Ina tsaye yau a gaban ku saboda akwai dama mai kyau dake Tahoe’s, zabe ya kusa, ban san ko ‘yan bindigan sun sani ba ko a’a, amma za mu basu notis. Ba zamu sassauta ba wurin kokarin ganin mun kawar da ta’addanci da kashe-kashe. Ina tabbatar muku hakan za mu bashi fifiko.”

- Yace.

Tinubu ya dira Kaduna, ya ziyarci Birnin Gwari

A wani labari na daban, Bola Ahmed Tinubu ya sauka a jihar Kaduna a ranar Litinin inda Gwamna Nasir El-Rufai ya tarbe shi.

Ya garzaya Birnin Gwari a mota inda ya jajantawa jama'ar da lamurran 'yan bindiga suka shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

iiq_pixel