Rikicin PDP: Wike da Ortom Sun Kauracewa Haduwa da Atiku a Filin Jirgin Makurdi
- Gabannin babban zaben 2023, an kasa warware rikicin cikin gida da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawar kasar
- Alaka na ci gaba da yin tsami tsakanin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP da tsagin Gwamna Nyesom Wike
- Gwamna Wike da takwaransa na Benue, Samuel Ortom sun yi watsi da Atiku a filin jirgin sama
Gabar da ke tsakanin dan takarar shugaban kasa na Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar da fusatattun gwamnonin jam'iyyar ya fito fili a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba.
Gwamna Samuel Ortom da takwaransa Nyesom Wike sun yi watsi da Atiku a lokacin da suka hadu a filin jirgin sama na Makurdi a jihar Benue.
Atiku ya yada zango a Benue a hanyarsa ya zuwa Nasarawa
Atiku ya hau jirgi zuwa jihar Benue a hanyarsa ta zuwa jihar Nasarawa don gudanar da yakin neman zabensa na shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, Channels TV ta rahoto cewa kimanin mintuna 20 kafin isowar Atiku, gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya isa filin jirgin saman.
Amma bayan mintuna biyar, wani jirgin sama dauke da dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP kuma Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya sauka a filin jirgin. Ya gaisa da Gwamna Ortom.
Jaridar Leadership ta kuma rahoto cewa an jiyo Ortom yana tambayar takwaransa na jihar Delta cewa "wato zaku shigo jihata ba tare da sanar dani ba?"
Wike da Ortom sun fice ba tare da sun jira Atiku da ke hanya ba
Ba da dadewa ba, wani jirgin dauke da gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya sauka. Ortom ya garzaya wajen don tarbarsa.
Gwamnonin sun rungume juna, suka yi gaisuwa sannan suka shiga motarsu suka fice.
Bayan minti 20 sai Atiki ya isa filin jirgin tare da tawagar kwamitin yakin neman zabensa da shugaban PDP na kasa.
Sai dai kuma, Gwamna Okowa da sauran yan jam'iyyar ne suka tarbe su; rashin Ortom da Wike a wajen ya tabbatar da cewar har yanzu basa ga maciji da juna.
Lamarin na zuwa ne kwana daya bayan Atiki ya ce ya gana da Gwamna Wike don magance rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar ba tare da mafita ba.
Da yake jawabi a ranar Lahadi, Atiku ya ce:
"Na gana da Wike sau biyu a Port Harcourt, sau biyu a Abuja, sau daya a Landan, ni da kaina."
Asali: Legit.ng