Kotu Ta Kwace Kujerar Shugaban Karamar Hukumar Chanchaga a Neja Jim Kadan Bayan Rantsar Dashi

Kotu Ta Kwace Kujerar Shugaban Karamar Hukumar Chanchaga a Neja Jim Kadan Bayan Rantsar Dashi

  • An gudanar da zabe, har an rantsar da shugaban karamar hukumar Chanchaga a jihar Neja, amma kotu ta soke zaben saboda wasu dalilai
  • An kwace kujerar shugaban karamar hukuma a hannun tsohon kwamishinan lafiya na jihar Neja bisa zargin an murda sunayen ‘yan takara
  • Kotun ta mayarwa Aminu Ladan nasarar tare da umartar a gaggauta rantsar dashi a matsayin shugaban karamar hukumar

Minna, jihar Neja - Wata babbar kotun Minna a jihar Neja ta kori Dr Mustapha Jibrin Alheri na jam’iyyar APC a matsayin shugaban karamar hukumar Chanchaga jim kadan bayan rantsar dashi.

Zaman kotun da mai shari’a Muhammad Muhammad ya jagoranta ya ayyana Yusuf Aminu Ladan a matsayin yardajjen dan takarar APC na karamar hukumar Chanchaga a zaben da aka yi na kanana hukumomi a jihar.

Kara karanta wannan

Zamba: Kotu Ta Hukunta Tsohon Ministan Buhari, Ta Yi Umurnin Kama Shi Da Garkame Shi a Kurkuku

Yusuf Aminu Ladan ya tunkari kotun ne bayan da ya zargi an sauya sunansa cikin ‘yan takara a zaben fidda gwanin da aka gudanar a wata Oktoba a karamar hukumar, Tribune Online ta ruwaito.

An kori zababben shugaban karamar hukumar Chanchaga a Neja
Kotu Ta Kwace Kujerar Shugaban Karamar Hukumar Chanchaga a Neja Jim Kadan Bayan Rantsar Dashi | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Yadda zaman kotu ya kaya a shari’ar APC da Aminu Ladan

Bayan duba cikin tsanaki, mai shari’a Muhammad ya ce ya fahimci koken Ladan, ya kuma gano cewa, APC ta mika sunan Dr Alheri ne hukumar zabe ta NSIEC ba bisa ka’ida ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, bisa dogaro da hujjojin da aka gabatar a gaban kotun, Dr Alheri na daga cikin masu ruwa da tsakin da suka jagoranci zaben fidda gwanin karamar hukumar, inda aka zabi Ladan a matsayin dan takarar yarjejeniya.

Matakin da kotu ta dauka

Kotun ta umarci hukumar ta NSIEC da ta ba da takardar shaidar komawa takara ga Ladan tare da janye ta Dr Alheri, rahoton jaridar BluePrint.

Kara karanta wannan

Ribadu: Dalilin da Yasa ba Zan Kai Binani har Kotun Koli ba Kan Zaben Fidda Gwani

Hakazalika, ta umarci da majalisar zartaswar jihar ta Neja da ta rantsar da Ladan a matsayin shugaban karamar hukumar Chanchaga.

A bangare guda, majalisar zartaswar jihar tuni ta rantsar da shugabannin kananan hukumomi 25 na jihar da aka zaba a zaben da aka kammala, ciki har da Dr Alheri.

A tun farko an gudanar zaben fidda gwanin ne a watan Oktoban bana, inda Ladan ya zargi an murda tare da sauya sunansa.

Ba wannan ne karon farko da kotu ke rushe zabe ba a wasu jihohin kasar nan, hakan ya faru a jihohi da dama cikin shekarar nan.

Kwanakin baya ne aka soke zaben kanan hukumomin da aka gudanar a jihar Osun saboda wasu dalilai na murdiya a zaben fidda gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.