Gwamna El-Rufai Ya Jero Abubuwa 2 da Za Su Hana Shi Zama Sanata Bayan Barin Mulki

Gwamna El-Rufai Ya Jero Abubuwa 2 da Za Su Hana Shi Zama Sanata Bayan Barin Mulki

  • Idan sun zo karshen mulkinsu, Gwamnoni sun saba neman takarar Majalisar dattawa a Najeriya
  • Gwamnan jihar Kaduna yace ban da shi a wannan babi domin bai da hakuri yin aikin Sanatoci
  • Malam Nasir El-Rufai ya fi sha’awar aiki a bangaren zartarwa inda shi ne yake da wuka da nama

Kaduna - A ranar Litinin, 12 ga watan Disamba 2022, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna babu shi babu zuwa majalisar tarayya ta kasa.

An san Gwamnoni da yin takarar Sanata idan sun gama wa’adinsu a jihohi, The Nation ta rahoto Malam Nasir El-Rufai yana cewa ya sha bam-bam.

Mai girma Nasir El-Rufai yace bai da hakuri da jajircewar da ake bukata wajen aikin majalisa.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron ‘yan majalisa da cibiyar nazarin aikin majalisa da damukaradiyya watau NILDS ta shirya.

Kara karanta wannan

Yadda Wani Gwamnan Najeriya Ya Baje Kolin Girki, Ya Rangada Miyar Farfesun Kifi

El-Rufai yace aikin majalisa akwai tsauri

Rahoton yace an yi taron ne safiyar Litinin, tsohon Ministan na birnin tarayya Abuja yake cewa ya san ba zai iya yin aikin da ‘yan majalisa suke yi ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

El-Rufai
Gwamna El-Rufai Hoto: @GovKaduna
Asali: UGC
“Majalisa wani bangaren gwamnati ne da na san ba zan taba iya aiki ba. Hakurin da ba mu da shi, shi ne kokarin samun goyon bayan a goyi-bayan kudirinka.
Gudanar da shugabanci a bangaren zartarwa kai-tsaye ne; abin mataki-mataki ne, da zarar kai ne Gwamna a jiha, to shikenan sai yadda ya ka ce ayi, za ayi.
Amma a majlisa, kusan duk daya ake, babu wanda ya fi wani. Hakan ya sa babu jagorancin da yake da wahala kamar ga wadanda kuke duk daya da su."

- Malam Nasir El-Rufai

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Malamin Musulunci Ya Rasu Watanni 2 da Yin Hasashen Zai Bar Duniya

An gaishe da Lawan da Gbajabiamila

The Nation tace El-Rufai ya yabi jagorancin Dr. Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila a kan irin cigaban da suka kawo kasar nan a lokacin mulkinsu.

"Ba na yi wa shugaban majalisar dattawa ko na wakilai hassada domin kusan aikinsu shi ya fi na kowa wahala a kasar nan.
A wajen zartarwa, za ka iya daukar aiki kuma kayi kora. Na san abokan aikinmu Gwamnoni da yawa za su tare a Majalisa.
Ina mai tabbatar maku da ba zan taba komawa majalisa ba domin ban tunani zan iya aiki a can."

- Malam Nasir El-Rufai

An kona ofishin PDP a Gombe

Labari mara dadin da magoya bayan PDP da masu kaunar damukaradiyya za su tashi da shi a yau shi ne kona ofishin kamfen jam’iyyar adawa a Gombe.

A wani jawabi, Mataimakin Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben Atiku/Dan Barde yace ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ne suka yi masu ta’adin.

Kara karanta wannan

Iyalai A Nigeria Na Hakura Da Ci Su Koshi Sabida Yanayin Tashin abinci

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng