Ba Abinda Zai Hana Bola Tinubu Zama Shugaban Kasa a 2023, Babban Fasto

Ba Abinda Zai Hana Bola Tinubu Zama Shugaban Kasa a 2023, Babban Fasto

  • Wani Babban Malamin Coci a jihar Legas yace babu abinda zai dakatar da Tinubu daga zama shugaban kasa a 2023
  • Fasto Adamu David Tunji, ya shawarci CAN ta sauya banzan tunaninta domin ba wanda zai iya maida Najeriya kasar Musulunci
  • Yace a tunaninsa Tinubu ba zai iya yakar Musulunci ba maimakon haka zai tallafa masa saboda matarsa da 'ya'yansa

Lagos - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC, Alhaji Bola Tinubu ne zai lashe babban zaɓen 2023 duk da yana takara Musulmi da Musulmi, inji Fasto Adamu David Tunji.

Babban Malamin a Majami'ar Christ Apostolic (CAC) dake Agbala Itusile, yankin Abule Egba ta jihar Lagos, yace babu abinda zai dakatar da Tinubu duk da sukar da yake sha daga wasu ɓangarori.

Bola Ahmed Tinubu.
Ba Abinda Zai Hana Bola Tinubu Zama Shugaban Kasa a 2023, Babban Fasto Hoto: thenationonlineng
Asali: Getty Images

Jaridar The Nation tace Babbam Malamin Cocin ya yi kira da ƙungiyar mabiya Addinin Kirista ta ƙasa (CAN) ta cire tsoro, a cewarsa ba wanda ya isa ya maida Najeriya ƙasar Musulunci.

Kara karanta wannan

Ina Tinubu Ya Ga Kafasitin Da Zai Mulki Nigeria, Yaje Ya Huta Kawai Inji PDP

A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Malamin yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Matar Tinubu Fasto ce a Cocin RCCG, duk wanda zai iya barin matarsa ta kai wannan matsayin ba zai yaƙi Kiristanci ba. A tunani na idan ya zama shugaban ƙasa zai taimaka wa Kiristoci kamar yadda ya wa matarsa da 'ya'yansa."

Fasto Tunji yace mataimakin shugaban ƙasa ba shi da zaɓi sai na Uban gidansa. Ya bayyana cewa ɗauko Shettima ba kamar yadda mutane ke yaɗa wa bane cewa za'a ƙasƙantar da Kiristanci.

A cewarsa 'yan Najeriya sun fara fahimta kuma ya roki masu kaɗa kuri'a kar su kuskura su damu da batun addini yayin zaɓar wanda ya kwanta masu a rai.

Yace:

"Kiristoci da Musulmai ba zasu iya kawar da junansu ba, muna auratayya mu yi kasuwanci tare kuma mu yi karatu tare. Ba wanda zai je kasuwa ya nuna damuwa kan mai saye ko mai sayarwa Musulmi ne ko kirista."

Kara karanta wannan

Babban Abinda APC Zata Yi Ta Lashe Zabe a 2023, Shugaba Buhari Ta Fasa Kwai

"Saboda me kuma zamu sa damuwa idan aka zo batun siyasa?"

Ya yi kira ga shugabannin Majami'u su sauya daga gurɓataccen tunanin da suke kai domin hakan ne ya sanya suke wasa da damarsu Musulmai na amfani da ita.

Wike ya caccaki masu sukar takara Musulmi da Musulmi

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Fara Ƙalaman Nuna Wanda Zai Mara Wa Baya Tsakanin Atiku da Tinubu a 2023

A wurin taron Addu'a da aka shirya wa PDP reshen jihar Ribas, gwamna Wike yace masu sukar tikitin Musulmi da Musulmi bai kamata su amince ɗan arewa ya gaji Buhari ba.

Gwamnan, wanda ke takun saƙa da Atiku Abubakar, ɗan takarar PDP, yace ba zasu kauracewa ɗan kudu su rungumi ɗan arewa ya ci gaba da mulki ba bayan ɗan arewa ya yi shekara 8.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262