Gwamna Wike Ya Nuna Alamun Wanda Zai Mara Wa Baya Tsakanin Atiku da Tinubu
- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace masu sukar takarar Musulmi da Musulmi ba su son gaskiya
- Wike, jagoran G5 yace duk waɗanda ke Allah wadai da tikitin APC sune kuma suke kokarin kare mulki ya ci gaba da zama a arewa
- Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin tsagin Wike da Atiku, ko a jiya Tambuwal ya gana da Ortom
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace ba bu wata gaskiya da za'a kare game da yunkurin ganin mulki ya ci gaba da zama a arewacin Najeriya a 2023.
Gwamnan ya roki masu sukar tikitin musulmi da musulmi da natsu su sake tunani kan tsarin mulkin karba-karba tsakanin kudu arewa a kujerar shugaban ƙasa.
Wike yace masu ikirarin ƙasar nan ba zata gamsu da tikitin Musumli da Musulmi ba ya kamata su samu zarrar yaƙar watsi da tsarin karba-karɓa na jam'iyyar PDP.
Gwamnan, wanda ke takun saƙa da Atiku, ya yi wannan jawabin ne a wurin taron Addu'a da aka shirya domin PDP reshen jihar Ribas, wanda ya gudana a Cocin Anglican, Patakwal.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar The Nation ta rahoto Wike na cewa:
"Kuna wasa da tunanin mutane, kun ce Najeriya ba zata cika ƙasa ɗaya ba idan aka bar Tikitin Musulmi-Musulmi, na yarda amma kuna ganin Najeriya ta gamsu idan mulki ya zauna a yanki ɗaya?"
Gwamnan ya ƙara da cewa ya kamata masu sukar takarar Musulmi da Musulmi su sani cewa 'yan Najeriya ba su goyon bayan mulki ya zauna a arewa bayan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Yace:
"Mafi yawanku kuna zaune ne, baku tambayar kanku, wasu na ta ɓaɓatu baku tambayesu ba, na yarda da abin kuke cewa, amma ku duba jam'iyyar ku na kokarin kai mulki yankin da Buhari ya fito, wake yaudarar wani anan?"
Daga karshe gwamnan ya tunasar da mambobin Cocin bukatar su fito su ba da gudummuwarsu a harkokin zaɓe.
Tambuwal ya gana da Ortom a Makurdi
A wani labarin kuma Gwamnan Aminu Tambuwa ya kai ziyara ga Samuel Ortom, Gwamnan Benuwai wanda ke tsagin Wike
Tambuwal, darakta janar na kwamitin kamfen Atiku yace ya je wurin Ortom ne domin duba hanyar da za'a kawo karshen taƙaddamar da ta hana PDP zaman lafiya.
Da yake jawabi, Tambuwal yace rikicin da mutane ke ganin yana faruwa a PDP ba yaki bane, saɓanin ra'ayin siyasa ne da zasu warware shi nan ba da jimawa ba.
Asali: Legit.ng