Kwankwaso Ya Nada Manyan Tsoffin Hadiman Ganduje Don Jagorantar Yakin Neman Zaben Gwamnan NNPP a Kano
- Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya saka manyan mutanen Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a tawagar yakin neman zabensa
- Tsoffin hadiman gwamnan jihar Kano sun samu mukamai a kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamna na New Nigeria Peoples Party (NNPP)
- Ana ganin wannan ci gaban zai shafi damar da jam’aiyyar APC da Bola Tinubu ke da shi a jihar a zabe mai zuwa
Kano - Manyan tsoffin hadiman Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, guda biyu sun samu mukamai a kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamnan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Kano, Daily Trust ta rahoto.
Wadanda aka ba mukami a kwamitin NNPP sune Ali Makoda, tsohon shugaban ma’aikatan Ganduje da kuma Muhuyi Magaji Rimingado, dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na jihar wanda ya nemi takarar gwamna a PDP bayan barin APC.
An bayyana mukaman da za su hau
Yayin da aka nada Makoda a matsayin Darakta janar na kwamitin kamfen din NNPP, an nada Rimingado wanda ya sanar da komawarsa jam'iyyar a matsayin darakta mai kula da tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta rahoto cewa yayin da Gwamna Ganduje ke goyon bayan mataimakinsa, Nasir Yusuf Gawuna a matsayin dan takarar APC, tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso na goyon bayan surukinsa, Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a zaben gwamnan Kano.
Masana harkokin siyasa da dama sun ce zaben gwamnan 2023 a jihar zai iya zama maimaicin abun da ya faru a zaben 2019 inda Ganduje ya yi nasara bayan an kaddamar da zaben a matsayin ba kammalalle ba da kuma sake sabon zabe.
Amma rikicin da ya dabaibaye APC kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar ya sa wasu masu ruwa da tsaki da dama ficewa daga jam’iyyar yayin da wasu suka shigo daga wasu jam’iyyun.
Manya daga cikin wadanda suka bar APC sun hada da Makoda, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Alhassan Rurum, wanda ya kasance dan majalisar tarayya mai ci da tsohon dan majalisar tarayya, Kawu Sumaila; da kuma Rimingado wanda ya fice tun bayan da ya raba jiha da gwamnan.
Hakazalika tsohon na hannun daman Kwankwaso kuma tsohon SSG, Rabiu Suleiman Bichi, ya dade da barin tafiyar Kwankwasiyya sannan ya koma tsagin Ganduje kuma a yanzu shi ke jagorantar yakin neman zaben APC a jihar.
Wata majiya a NNPP ta bayyana cewa zaban Makoda da Rimingado da aka yi wata dabara ce don cimma nasara.
Ya kara da cewar suna sane cewa Rimingado ya taka irin wannan rawar ga APC a zaben 2019 amma ba a hukumance ba.
Zan tabbatar da ganin nasarar NNPP a zabe mai zuwa
Da yake tabbatar da nadin nasa, Rimingado ya ce koda dai ba a tuntube shi ba kafin a bashi mukamin, ya yanke shawarar karbar lamarin saboda ya nuna cewa jam’iyyar na mutunta gudunmawar da yake bata.
Dalilin da Ya Sa Nake Goyon Bayan Tinubu Duk Ba Jam'iyyar Mu Ɗaya Ba, Sanatan PDP Ya Faɗi Abinda Ya Hango
Ya kuma ce zai yi iya bakin kokarinsa don tabbatar da nasarar jam’iyyar duk da cewar bai riga ya mallaki katin shaidar zama dan jam’iyyar ba.
Kungiyar Arewa ta ce babu ita babu zaben APC a 2023
A wani labarin, wata kungiyar kare muradun arewa ta yi ikirarin cewa al'ummar yankin arewacin Najeriya ba za su sake zaban APC ba a 2023 domin sun sha bakar wahala.
Jagororin kungiyar sun ce zaban APC a zabe mai zuwa tamkar kashe kai da kai ne don an sha bakar wuya a shekaru takwas da tayi tana mulki.
Asali: Legit.ng