Dalilan da Suka Sa Nake Goyon Bayan Tinubu Duk Ba Jam'iyyar Mu Daya Ba, Sanatan PDP

Dalilan da Suka Sa Nake Goyon Bayan Tinubu Duk Ba Jam'iyyar Mu Daya Ba, Sanatan PDP

  • Sanata Chimaroke Nnamani, yace yana bayan Bola Tinubu ne saboda son ci gaba ga al'ummar kudu maso gabas
  • Tsohon gwamnan jihar Enugu, mamban jam'iyyar PDP ya jima yana nuna goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC
  • Jam'iyyar sanatan watau PDP, ta tsaida Atiku Abubakar a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2023

Enugu - Tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani, yace yana goyon bayan ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu, ne saboda kishin kudu maso gabas.

The Cable ta ruwaito cewa ya faɗi haka ne a wurin bikin kaddamar da kodinetocin ƙungiyar magoya bayan Tinubu/Shettima masu zaman kansu (ICC) na jiha da kananan hukumomi a Enugu ranar Asabar.

Chimaroke Nnamani.
Dalilan da Suka Sa Nake Goyon Bayan Tinubu Duk Ba Jam'iyyar Mu Daya Ba, Sanatan PDP Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Sanatan wanda ke kan madafun iko kuma mamba a jam'iyyar PDP yace ba ya goyon bayan Tinubu don kwaɗayin wani mukami da zai samu na ƙashin kansa.

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Gwamna, Shugaban Matasan PDP Na Shiyya da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC

Yace tsohon gwamnan jihar Legas ɗin yana da kwarewar iya aiki da zai iya saita Najeriya, inda ya ƙara da cewa kamata ya yi Ibo su yi amfani da shi su gina masa goyon baya a sassan kasar nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ba wai ina hangen kujerar Minista bane saboda na riga na wuce nan, muna yin wannan abun ne domin ƙauna da kishin mutanen mu.
"Ndigbo zasu yi amfanin da goyon bayan Tinubu da APC a 2023 ne domin kawo ci gaba a sassan ƙasar nan. Kar ku damu da masu zagi, ku maida hankali kan manufarku domin ita ta fi muhimmanci."

- Chimaroke Nnamani.

Nnamani ya jima yana bayyana goyon bayan Tinubu a fili duk da ya kasance mamban babbar jam'iyyar hamayya watau PDP.

Yace duk cikin gwamnonin da suka ɗare kan madafun iko bayan dawowar mulkin Demokuraɗiyya a 1999, Bola Tinu ne kan gaba wurin kawo ci gaba.

Kara karanta wannan

Atikun Ba Wata Barazana Da Zaiwa Tinubu A Arewa Maso Gabas - Bayero

A cewarsa, Tinubu ya haɗa tawaga mai ƙarfi masu kwakwalwa a kowa ne ɓangare lokacin da ya lashe zaɓen gwamnan Legas, Punch ta rahoto.

Atiku Ya Zakulo Wani Gwamna Mai Ci, Ya Naɗa Shi Babban Mukami a Kwamitin Kemfen PDP 2023

A wani labarin kuma mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar PDP ya ƙara sabbin naɗe-naɗe a kwamitin kamfensa

A wata sanarwa da gwamna Aminu Tambuwal, Darakta Janar na kamfen Atiku ya fitar, yace PDP-PCO ta amince da naɗa sabon gwamnan Osun a matsayin mamban kwamitin.

Baya ga Adeleke, Tambuwal ya sanar da wasu muhimman naɗe-naɗe a yakin neman zaɓen Atiku duk a shirin tunkarar babban zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel