Abun da Tinubu Ya Fada ma Shugabannin Musulunci Kan Zaben 2023
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin addinin musulunci daga yankin kudu maso yammacin Najeriya
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023 ya bukaci shugabannin addini da su nusar da mabiyansu muhimmancin fitowa su zabi wadanda suka cancanta
- Tinubu ya yi kira ga yan Najeriya a kan su lura domin ana lokacin zabe da wasu yan siyasa ke amfani da karya da yaudara
Oyo - A ranar Lahadi, 11 ga watan Disamba, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ya ba yan Najeriya tabbacin cewa zai zamo mai gaskiya da adalci ga kowa.
Tinubu ya bayar da tabbacin ne yayin da yake jawabi a wani taro da shugabannin Musulunci daga kudu maso yamma a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, rahoton PM News.
Dan takarar na APC ya yaba ma shugabannin addini a kasar kan addu'o'i da suke ci gaba da yi a kasar, wanda ya taimaka wajen hadin kai da zaman lafiya da aka samu a tsakani.
Da yake magana kan babban zabe mai zuwa, Tinubu ya bukaci malaman Musulunci da su ilimantar da mabiyansu kan muhimmancin sauko hakkin da ya rataya a wuyansu da zabar yan takarar da ke da tarihi mai kyau a aikin gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kada ku yarda a yaudare ku da karya, Tinubu ga yan Najeriya
Tinubu ya kuma bukace su da kada su fada tarkon karya da yaudara na wadanda basu da wani abun gabatarwa.
Tinubu wanda ya yi wasu daga cikin maganganunsa a harshen Yarbanci ya ce:
"Wannan lokaci na zabe lokaci ne na dunkule gaskiya da karya. Ina son zaben ya kasance a kan turba ta gaskiya.
"Menene tarihin kokarin dan takara kuma menene manufofinsa? Na nemi ku bukaci magoya bayanku da su fito sannan su yi zabe kuma su yi hakan cikin hikima. Ku zabi yan takara masu hangen nesa don ci gaba da zaman lafiya Najeriya ta yadda kundin tsarin mulkinmu da yancin doka zai kasance bisa juriya da tausayi."
Ya kuma ba yan Najeriya tabbacin cewa zai zamo shugaba mai gaskiya da adalci yana mai cewa:
"Alkawarin da na dauka na yin gaskiya da adalci ya yi daidai da ka’idojin addinin Musulunci.
"An bukaci Shugaba a irin wannan alkarya tamu ya zamo shugaba mai adalci ga kowa. Idan aka zabe ni, zan yi shugabanci cikin gaskiya da damokradiyya daidai da kudin tsarin mulkin kasarmu."
Tinubu ya bayyana tanadin da ya yiwa kasar idan aka zabe shi
Da yake nuni ga aikinsa a matsayin gwamnan jihar Lagas, Tinubu ya yi alkawarin amfani da wannan gogewar wajen jagorantar Najeriya don daukaka kasar da sabonta fatan yan Najeriya.
Kan tsaro, Tinubu ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci, sace-sacen mutane da sauran laifuka ta hanyar daukar karin jami'ai da za a horar, baya ka samar da karin kayayyakin aiki na tsaro don yakar miyagu.
Game da tattalin arzikin kasar, Tinubu ya ce zai bunkasa ta tare da sauya fasalinta zuwa ga cimma akalla karin kaso 6 duk shekara, rahoton The Cable.
Ya ce za a cimma wadannan manufofin ne ta hanyar gyara manufar kasuwancinmu, inganta ababen more rayuwa, sabbin hanyoyin samar da wutar lantarki da kuma gagarumin sauyi a kasafin kudi.
Game da ma'aikatar noma, Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da tsaron abinci ta hanyar inganta kayan aikin noma don tabbatar da ganin cewa babu dan da ya kwanta da yunwa.
Asali: Legit.ng