Hotunan Ziyarar da Seyi Tinubu da Matasan APC Suka Kaiwa Buhari har Daura
- Seyi Tinubu, ‘dan Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar APC ya ziyarci Buhari
- Seyi ya kwashi tawagar kwamitin matasa ba tawagar kamfen din Tinubu da Shettima har garin Daura inda suka kai gaisuwa ga Buhari
- A watan Nuwamban da ta gabata, Seyi ya jagoranci tattakin mutum miliyan daya da aka yi a Kano na nuna goyon baya ga Tinubu da Shettima
Daura, Katsina - Seyi, ‘dan Bola Tinubu, ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, a ranar Asabar ya jagoranci wasu wakilai inda suka ziyarci shugaban Muhammadu Buhari.

Source: UGC
Shugaban kasan a halin yanzu yana garin Daura dake jihar Katsina, jaridar TheCable ta rahoto.
Wakilan sun hada da mambobin kwamitin matasa na kwamitin kamfen din Tinubu da Shettima.

Kara karanta wannan
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Zai Shilla Kasar Amurka Gobe Lahadi, Zai Kwashe Mako 1
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A watan Nuwamba, matashin Tinubu ya jagoranci wani tattakin kara a jihar Kano inda magoya bayan ‘dan takarar shugaban kasa suka fito kwan su da kwarkwatarsu.
Kalla hotunan ziyarar da suka kai wa Shugaba Buhari:

Source: UGC

Source: UGC

Source: UGC

Source: UGC
Asali: Legit.ng