Tsohuwar Minista a Mulkin PDP Ta Jingine Atiku, Ta Bayyana Zabinta a 2023

Tsohuwar Minista a Mulkin PDP Ta Jingine Atiku, Ta Bayyana Zabinta a 2023

  • Tsohuwar ministar ilimi a Najeriya, Obiageli Ezekwesili, tace Peter Obi ya sha gaban sauran 'yan takara a zaɓen 2023
  • Ezekwesili, tsohuwa mataimakiyar shugaban bankin duniya na Afirka tace ba zata tsallake Obi ta zabi Atiku ko Tinubu ba
  • Tun bayan sauya sheka da kuma tsayawa takarar shugaban ƙasa a LP da Obi ya yi, ana ganin yana cikin 'yan takara na sahun gaba

Abuja - Tsohuwar ministan ilimi (2006-2007), Dakta Obiageli Ezekwesili, tace ba zai yuwu ta tsallake ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party, Peter Obi, ta zaɓi wani daban ba a 2023.

Tace manyan 'yan takara uku da ake ganin sune a sahun gaba, za'a iya ɗora su a Sikeli da iyakacin bayanan da kowa ya sani kuma bayan ta yi nata gwajin ta gano cewa Obi ya shiga gaban dukkanin 'yan takara.

Kara karanta wannan

Muna tare da CBN kan dokar kayyade cire kudi: Kungiyar Matasa

Obiageli Ezekwesili
Tsohuwar Minista a Mulkin PDP Ta Jingine Atiku, Ta Bayyana Zabinta a 2023 Hoto: Obiageli Ezekwesili
Asali: Depositphotos
"Game da batun masu neman zama shugaban ƙasa, abinda nace kuma zan maimaita a ko ina, na ɗora manyan 'yan takara 2 a Sikeli da iya abinda na sani haka kuma na ɗauki mutum uku na sahun gaba na ɗora su."
"Bayan na gama da duk wani bincike na da tantancewa, ba bu ta yadda zan bar Peter Obi, na zaɓi ɗaya daga cikin manyan 'yan takara guda biyu (Atiku da Tinubu)."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Cewar Ezekwesili yayin da ta bayyana a cikin shirin Channels tv.

Ezekwesili, tsohuwar mataimakiyar shugaban Bankin duniya a Afirka tace binciken abinda ka iya faruwa a 2023 ya nuna cewa canji mai ƙarfi na nan zuwa daga ɓangaren matasa.

A cewarta idan ka duba Matasa ke da kaso 60 cikin 100 na yawan kuri'u kuma da yawansu suna goyon bayan takarar tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Ku Maida Takardun Kudi Mara Fenti Bankuna, Gwamna Ya Bayyana Abinda Zai Faru Nan Gaba

Ta ƙara da cewa mata ke da kaso 51 na kuri'u kuma sun karkata wajen ganin Obi ya karbi madafun iko. Tace Peter Obi ya ratsa lungu da sako na ƙasar nan don yaɗa manufar tafiya da kowa a gwamnati, The Cable ta tattaro.

Mambobin majalisar dokokin Gombe biyu sun koma NNPP

A wani labarin kuma Kwankwaso Ya Ƙara Ƙarfi, Manyan 'Yan Majalisu Biyu Sun Fice APC zuwa jam'iyyar NNPP mai kayan marmari

Mambobin majalisar dokokin jihar Gombe, Hamza Adamu da Bappa Usman, sun bayyana cewa sun bar APC zuwa NNPP ne domin cigaban al'umma da jiharsu.

Wannan lamarin dai ya ɗaga jam'iyyar NNPP, wacce Kwankwaso ke takarar shugaban ƙasa zuwa matsayin babbar jam'iyyar adawa a Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262