Ku Maida Tsoffin Takardun Kuɗi Bankuna Tun Wuri, Gwamnan CBN

Ku Maida Tsoffin Takardun Kuɗi Bankuna Tun Wuri, Gwamnan CBN

  • Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya yi kira ga 'yan Najeriya su maida takardun kuɗin dake hannunsu yanzu zuwa Bankuna
  • Jim kaɗan bayan ganawa da Buhari kan lamarin, gwamnan yace kuɗin zasu cigaba da amfani zuwa 31 ga watan Janairu
  • A cewarsa daga ranar duk wata takardar kuɗi mara Fenti ba zata sake moruwa ba a Najeriya

Daura, Katsina - Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bukaci 'yan Najeriya su maida takardun kuɗin da suke hada-hada dasu yanzu zuwa bankuna tun kafin lokaci ya ƙure.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labaran gidan gwamnati ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba, 2022.

Takardun kuɗin Najeriya.
Ku Maida Tsoffin Takardun Kuɗi Bankuna Tun Wuri, Gwamnan CBN Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Emefiele ya zanta da yan jarida ne jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari kan harkokin da suka shafi CBN da Tattalin arziki a Daura, jihar Katsina.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa a ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba, 2022, shugaba Buhari ya bayyana sabbin takardun kudin Naira da aka sauya wa fasali.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Takardun kuɗin da sauyin ya shafa kuma aka bayyana wa yan ƙasa a wannan rana sun haɗa da N200, N500 da N1000.

Sai dai matakin sauya tsarin takardun kuɗin ya ta da ƙura sosai a sassan ƙasar nan yayin da masana suka ci gaba da jaddada cewa hakan zai shafi tattalin arziƙi.

Da yake jawabi ga masu ɗauko rahoto daga gidan gwamnati ranar Alhamis (Yau), gwamnan CBN yace tuni Bankuna suka fara baiwa mutane sabbin kuɗin da suka isa gare su ranar Laraba.

"Ina mai tabbatar muku zasu karaɗe ko ina, kowa ya kwantar da hankalinsa, tsofaffin takardun zasu cigaba da amfani har zuwa 31 ga watan Janairu, 2023."

"Nima bari na taba wasan barkwanci, baki ɗaya takardun kuɗin da aka wa Fenti (sabbi) da marasa fenti (tsoffi) zasu ci gaba da yawo tsakanin mutane."
"Amma daga ranar 31 ga watan Janairu, marasa Fantin nan ba zasu ƙara amfani ba, saboda haka ina rokonku da ku maida su banki tun kafin lokaci ya kure."

- Godwin Emefiele.

Majalisar Wakilai Ta Umarci CBN ta Dakatar da Tabbatar da Sabbin Tsarikan Kayyade Cire Kudi Ɗaga Banki

A wani labarin kuma Majalisar Wakilan tarayya ta kai ruwa rana a zaman mambonta game da sabon tsarin takaita yawan kudin cirewa duk rana

Majalisar ta kuma nemi babban bankin Najeriya ya dakatar da sabon tsarin kana gwamnan CBN ya bayyana gabanta don yin ƙarin haske.

A cewar majalisar idan har aka tabbatar da tsarin, to kananan yan kasuwa zasu durkushe sakamakon rashin isassun kuɗin da zasu tafiyar da harkokinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel