‘Yan Najeriya Su Shiryawa Takarar Kirista-Kirista, Babu Musulmi Inji Mai dakin Tinubu
- Sanata Oluremi Tinubu tayi jawabi na musamman a taron da jam’iyyar APC ta shiryawa mata
- Matan APC na yankin Kudu maso yammacin Najeriya sun yi gangamin Tinubu/Shettima a Legas
- Oluremi Tinubu tace takarar Mai gidanta tare da Musulmi ya bada damar a tsaida Kirista da Kirista
Lagos - Sanata Remi Tinubu tace akwai yiwuwar nan gaba a samu tikitin Kirista da Kirista a Najeriya tun da jam’iyyar APC ta bude wannan kofa a siyasa.
Vanguard ta rahoto Oluremi Tinubu a ranar Alhamis tana cewa an bada damar da Kiristoci zalla za su tsaya takara kamar yadda APC tayi wannan karo.
Uwargidar ‘dan takarar shugaban kasar na APC tayi wannan bayani sa’ilin da tayi wa mata jawabi a gangamin da jam’iyyar APC ta shirya dazu a garin Legas.
APC ta gudanar da taro na musamman domin matan yankin Kudu maso yammacin Najeriya. An shirya taron ne a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena.
Tinubu/Shettima za su kawo sauyi
A cewar Sanata Tinubu, idan Bola Tinubu da Kashim Shettima suka karbi mulkin kasar nan a 2023, to gaba daya za su canza yadda tsarin siyasa take.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanatar ta Legas ta tsakiya ta ba jam’iyyarta kariya a lokacin da ake sukar yadda aka tsaida Musulmi da Musulmi a zaben kasa mai jama'a dabam-dabam.
Tsohuwar uwargidar jihar Legas din tana ganin tun da yanzu an tsaida Musulmai biyu a APC, hakan zai bada dama Kiristoci zalla su samu tikiti gobe.
Wata rana za a ga tikiti babu Musulmi
"A game da tikitin Musulmi da Musulmi, wannan zai bada dama dama nan gaba, wata rana, mu samu tikitin Kirista da Kirista.
Abin da Ubangiji ya yi wa kasarmu abin ban mamaki ne."
- Sanata Oluremi Tinubu
Aisha Buhari ba ta je taron matan APC ba
Daily Trust tace Tinubu ta aika gaisuwarta ga Hajiya Aisha Buhari wanda ya kamata ta halarci taron siyasar matan na APC, amma sai ba ta samu zuwa ba.
An dade ana yin taro ba tare da matar shugaban kasar ba. Tinubu wanda Fasto ce, ta ji dadin yadda ta ga tarin mata a gabanta, suna goyon bayan mai gidanta.
Godwin Emefiele ya sa labule da Buhari
A ranar Alhamis ne aka samu rahoto Godwin Emefiele ya zauna da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi masa bayani kan tsarin takaita canjin kudi.
Emefiele yace ya wajaba a rage adadin kudin da jama’a suke cirewa, ya kuma yi karin-haske kan sababbin takardun kudi da aka buga da sun fara fitowa.
Asali: Legit.ng