2023: An Tona Asirin Fitaccen Ɗan Takarar Shugaban Kasa, An Gano Atiku Yake Wa Aiki
- An yi ikirarin cewa jam'iyyar Labour Party da ɗan takararta na shugabn kasa wani reshe ne na jam'iyyar PDP duk abu ɗaya ne
- Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar SDP, Adebayo Adewole ne ya faɗi haka, yace sun so kulla kawance da LP
- Peter Obi na jam'iyyar LP na ɗaya ɗaga cikin yan takara na sahun gaba a zaɓen 2023, kuma shi ne abokin takarar Atiku a zaɓen 2019
Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Adebayo Adewole, yace jam'iyyar Labour Party da PDP duk ɗayane basu da banbanci.
Adewole ya yi wannan ikirarin ne yayin hira a cikin shirin Sunrise Daily na gidan Talabijin ɗin Channels ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba, 2022.
"Jam'iyyar LP reshe ne na PDP uwarsu ɗaya," A cewarsa yayin da yake bayanin cewa jam'iyyarsa watau SDP ta so yin maja da LP da wasu jam'iyyu.
"Mun yi kokarin maja da jam'iyyar PRP da kuma Labour Party lokacin tana a matsayin jami'iyya mai cin gashin kanta," Inji Adewole a rahoton Sahara Reporter.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar PDP, Peter Obi, shi ke rike da tikitin takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya na LP a 2023.
Wane alƙawurra Adewole ya ɗaukarwa 'yan Najeriya?
Ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP ya ɗauki alƙawarin fatattakar Talauci a Najeriya idan har 'yan kasa suka kaɗa masa kuri'unsu ya kafa gwamnati a 2023.
"Meyasa ake fama da talauci? Ba wai talaucin rashin biliyoyin Naira a Asusu ya fi damun mutane ba, 'yan Najeriya na fama da talaucin da idan suka wayi gari da safe, ba su da abinci mai tsafta ko babu abincin kwata-kwata."
"Ba su da tsaftataccen mahalli ko wuraren kula da lafiya da kuma ilimi, yanzu ka faɗa mun wanne ne daga cikin waɗanda ba zai wadata ba a cikin shekaru biyu?"
- Adebayo Adewole.
Babbar Kotu Ta Rushe Dukkanin Zabukan Fidda Gwanin PDP a Jihar Ebonyi
A wani labarin kuma Babbar Kotun tarayya ta Abuja ta soke tikitin baki ɗaya 'yan takarar jam'iyyar PDP a Jihar Ebonyi
Mai shari'a Binta Nyako, yayin da take yanke hukuncin ranar Talata tace PDP ta saɓa wa hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara, ta gudanar da zaben ba tare da zartar da umarnin Alƙali ba.
Sai dai Mai shari'a Nyako ta baiwa babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa wa'adin kwanaki 14 ta shirya sabon zaben fidda gwani ko ta rasa 'yan takara a zaɓen 2023.
Asali: Legit.ng