PDP Ta Ba da Hutun Aiki Saboda Ziyarar da Atiku Zai Kai Jihar Anambra
- Jam’iyyar PDP ta ayyana ranar Alhamis ta sama a matsayin ranar hutu saboda ¬zuwan da Atiku zai yi jihar
- Atiku Abubakar zai kai ziyara jihar Anambra domin gudanar taron kamfen dinsa na takarar shugaban kasa
- Jiga-jigan PDP a jihar sun bayyana dalilin da yasa suke mutunta Atiku fiye da duk wani dan takarar shugaban kasa
Jihar Anambra - Jam’iyyar PDP da magoya bayan Atiku da Okowa a jihar Anambra za su yi hutun aiki a ranar Alhamis a wata ziyarar kamfen da Alhaji Atiku Abubakar zai kai jihar.
Wannan na fitowa ne daga cikin wata sanarwa a birnin Awka jihar Anambra a ranar Laraba bayan tattaunawar masu ruwa da tsaki da mambobin jam’iyyar da farfesa Obiora Okonkwo ya jagoranta.
An yi zaman tattaunawar ne domin zanta batutuwan da suka shafi shirin tarbar Atiku a jihar ta Anambra a mako mai zuwa, Punch ta ruwaito.
Mambobi da jiga-jigan jam’iyyar sun ware ranar 15 ga watan Disamba a matsayin ranar hutun aiki domin tarbar dan takararsu na shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mambobin jam’iyyar sun bayyana cewa, za su yi hakan ne domin nuna goyon bayansu ga Atiku a kokarinsa da shirinsa na ceto Najeriya.
Atiku masoyin jihar Anambra da mutanenta ne
Sanarwar da PDP ta fitar na dauke da sa hannun mataimakin daraktan yada labarai na tawagar kamfen Atiku-Okwa a jihar Anambra, Mr Uloka Chukwubuikem, kafar labarai ta Koko ta tattaro.
Sanarwar ta ce:
“Anambra gida ne ga Atiku Abubakar. Baya ga kasancewarsa surukinmu kuma yana ‘ya’ya da tsatsonsu Onitsha ne, tsawon shekaru ya nuna kauna da shawarsa ga jiharmu.
“Za mu iya tunawa a 2007 a lokacin Atiku Abubakar ya fito takawar a rusasshiyar jam’iyyar ACN, ya zabi Sanata Ben Ndi Obi daga Awka a matsayin abokin takara.
"A 2019, nan ma takanas ya zabi Peter Obi a matsayin abokin takara, duk da kuwa wasu shugabannin PDP sun ki hakan.”
Atiku ya samu kyakkyawar tarba a jihar Legas a lokacin da ya kai ziyarar kamfen.
Asali: Legit.ng