Peter Obi: ASUU Ba Zata Sake Shiga Yajin Aiki Ba Idan Na Zama Shugaban Kasa

Peter Obi: ASUU Ba Zata Sake Shiga Yajin Aiki Ba Idan Na Zama Shugaban Kasa

  • Peter Obi ya sha alwashin cewa idan har ya zama shugaban kasa ƙungiyar ASUU ba zata sake tafiya yajin aiki ba
  • A ranar Talata, Peter Obi ya gudanar da gangamin yakin neman zabensa a Owerri, babban birnin jihar Imo
  • Ana kallo tsohon gwamnan jihar Anambra a matsayin ɗaya daga cikin 'yan takara na sahun gaba a zaɓen 2023

Imo - Peter Obi, mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar LP, ya yi alƙwarin cewa ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta ƙasa (ASUU) ta zata sake shiga yajin aiki ba idan ya ci zaɓe a 2023.

The Cable ta ruwaito cewa Obi ya faɗi haka ne a wurin Ralin yakin neman zaɓensa wanda ya guda a Owerri, babban birnin jihar Imo ranar Talata.

Peter Obi.
Peter Obi: ASUU Ba Zata Sake Shiga Yajin Aiki Ba Idan Na Zama Shugaban Kasa Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan jihar Anambra yace goben kowace ƙasa ya dogara ne da Ilimi da Lafiya, inda ya jaddada cewa zai zuba jari mai tsoka a ɓangarorin biyu.

Kara karanta wannan

Wa Zaka Zaba Tsakanin Atiku da Peter Obi Idan Baka Cikin 'Yan Takara? Tinubu Ya Ba Da Amsa Mai Jan Hankali

Jaridar Punch ta ruwaito Obi na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Idan kuka zaɓe ni na zama shugaban kasa, Datti ya zama mataimakina, ASUU ba zasu ƙara tafiya yaji ba, zamu tattauna da su kuma zamu yi aiki tare da ɗalibai."
"Goben kowace ƙasa ya dogara ne da ilimin su da kuma ɓangaren lafiya, zan zuba jari mai gwaɓi idan kuka zaɓe mu."
"Haka kuma muna son koma wa kan Noma shiyasa muke son juya akalar Najeriya daga mai laƙume wa zuwa mai samarwa. Zamu samar da ayyukan yi ga yan ƙasa."

Peter Obi ya ƙara da cewa shi da abokin takararsa suna da tarihi mai kyau sakamakon sun rike muƙaman gwamnati a baya kuma babu wani kashi a bayansu.

"Ni da Datti ba 'yan rashawa bane, tarihin mu mai tsafta ne, Datti ya rike kujerar Sanata ni kuma na zauna kujerar gwamnan jihar Anambra. Idan kuna son ganin abinda na yi ku tafi Anambra."

Kara karanta wannan

Amarya Ta Yanke Jiki Ta Faɗi Yayin da Ango Ya Fasa Aurenta Ranar Biki, Bidiyon Ya Sosa Zuciya

Mutane Sun Yi Cikar Kwari Yayin Da Masari Ya Mika Tuta Ga Ɗan Takarar Gwamnan Katsina a 2023

A wani labarin kuma Gwamna Masari ya kaddamar da yakin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan Katsina a inuwar APC, Dikko Radda

Gwamna Masari, wanda wa'adin mulkinsa zango na biyu zai ƙare a 2023 ya miƙa wa ɗan takarr Tuta a wurin gangamin APC na farko da aka shirya a Faskari.

A wurin taron, Dikko Radda ya sha alwashin idan har Allah ya ba shi mulkin Katsina zai tsare rayuka da dukiyoyin al'umma iyakar ƙarfinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262