Rashin Tsaro Ya Ragu Sosai a Karkashin Mulkin Buhari, Inji Tinubu

Rashin Tsaro Ya Ragu Sosai a Karkashin Mulkin Buhari, Inji Tinubu

  • Dan takarar shugaban kasa na APC ya bayyana kadan daga nasarorin shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin shekaru 8
  • Tinubu ya ce Buhari ya kassara karfin ‘yan ta’adda a kasar nan, musamman a yankin Arewa masu Gabas
  • Tinubu ya kuma bayyana dalilin da yasa har yanzu sauran ‘yan ta’adda basu kare ba, kuma zai yi aikin tabbatar da sun kare

Landan, Burtaniya - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rage adadin faruwar ayyukan ta’addanci a Najeriya.

A fahimtar Tinubu, Buhari ya yi yaki da ayyukan ta’addanci a bangarorin kasar nan da dama tun lokacin da ya karbi Mulki a shekarar 2015, shekaru kusan 8 yanzu.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da BBC News da aka yada a ranar Talata 6 ga watan Disamba, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaba Buhari Ya Yi Kwanaki fiye da 200 a Asibiti, Ya Ziyarci Kasashe 40

Tinubu ya ce Buhari ya yaki 'yan ta'adda a kasar nan cikin shekaru 8
Rashin tsaro ya ragu sosai a karkashin mulkin Buhari, Tinubu | Hoto: Vanguard News
Asali: Facebook

Buhari ya yi kokari, saura kiris ‘yan ISWAP su kare, inji Tinubu

Da aka tambaye shi game da yanayin tsaro da kuma tsarin da zai zo dashi, sabanin na Buhari, Tinubu ya yaba da Buhari ya ce barnar ‘yan ta’adda ta ragu a mulkin Buhari, a cewarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ya ragu. Zan kare shi. A baya, kananan hukumomi 17 da kuma jihohi kusan hudu ne inda ‘yan Jihadi suka dasa tutocinsu a Najeriya. Yanzu babu wannan. Ya riga ya wuce.
“Faro rikici yana da sauki. Kawo zaman lafiya da gyara ya fi wahala. Ga mu nan dai yanzu, Buhari ya dakile amma ba wai daddale hallaka ‘yan ISWAP ba.
“Sai dai su yi maganan kananan makamai da alburusai da kayayyakin fasaha da zai taimaka wajen karasa kakkabe wadancan.
“Har yanzu Yammacin duniya bai gamsu da gwamnatin Buhari ba yadda ya kamata da har za a sayar mana da makamai da kayayyakin fasaha da ake bukata.

Kara karanta wannan

Shinkenan ta takewa Tinubu, 'yan jiharsa su bayyana dan takarar da za su zaba ba shi ba

Tinubu ya ce ba zai amince da tattaunawa da kowa ba sai an cika ka'idoji

Wannan ne karon farko da Tinubu ya amince da tattaunawa da 'yan jarida, domin yace ba zai yi muhawarar siyasa da sauran 'yan takara ba.

Tinubu ya ce sai Peter Obi ya cika wasu ka'idoji hudu kafin ya amince ya fito don tattaunawa dashi game da zaben 2023.

Ana ta kira ga 'yan siyas ada su yi muhawara da juna domin tabbatar da wanda yafi cancanta ya gaji kujerar Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.