Shagari: Kiristocin Arewa Ba Za Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, Za Su Juya Wa APC Baya

Shagari: Kiristocin Arewa Ba Za Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, Za Su Juya Wa APC Baya

  • Mukhtar Shagari, tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto ya ce kiristocin arewacin Najeriya ba za su zabi APC ba a 2023
  • Tsohon ministan albarkatun ruwan ya ce tikitin musulmi da musulmi da APC ta yi a matakin shugaban kasa cin fuska ne da raini ga kiristocin Najeriya
  • Shagari ya ce yan Najeriya yanzu sun waye don haka ba za su zabi APC ba da ya ce bata tsinana musu komai ba

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Mukhtar Shagari, ya ce jam'iyyar APC mai mulki a kasa ta yi wa kiristocin arewa laifi, gabanin babban zaben shekarar 2023, Vanguard ta rahoto.

Shagari ya bayyana hakan ne a hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television da wakilin Legit ya yi nazari.

Kara karanta wannan

Fata-fata Kenan: Jama'a Sun Dauki Dumi Bayan Ganin Wani Kalan Takalmi Da Peter Obi Ya Sanya A Wurin Taro

Muktar Shagari
Shagari: Kiristocin Arewa Ba Za Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, Za Su Juya Wa APC Baya. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, APC ta gaza kuma tikitin musulmi da musulmi da ta yi don zaben 2023 ba zai bata sakamakon da ta ke nema ba a arewa.

Ya ce:

"Kiristocin kasar nan, musamman na arewa suna jin a wulakanta su, suna ganin an ci mutuncinsu lokacin da APC ta yanke shawarar yin tikitin musulmi da musulmi."

Shagari, tsohon ministan albarkatun ruwa kuma mamba na kwamitin amintattu na PDP ya ce idan har dan takarar shugaban kasar na APC, Bola Tinubu, yana da mata kirista, ya kamata ya zabi abokin takara kirista.

Ya bayyana tikitin na addini guda a matsayin cin mutunci, ya kara da cewa kiristocin Najeriya za su juya wa jam'iyyar mai mulki baya a zaben shugaban kasa da ke tafe.

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Magantu Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na Tinubu Da Shettima

"Suna tunanin kiristoci da musulmin kasar nan sakarkaru ne. Sun yanke shawarar yin tikitin musulmi da musulmi, suna tunanin hakan zai saka kowa a arewa maso yamma, arewa maso gabad da sauran yan Najeriya za su amince amma yan Najeriya sun waye, sun san abin da suke so; suna son gwamnatin da za ta sauya rayuwarsu."

Sheikh Ibrahim Daimagoro ya ce tikitin musulmi da musulmi ba matsala bane

Sheikh Ibrahim Daimagoro, malamin addinin musulmi ya ce bai ga wani matsala da tikitin musulmi da musulmi ba na jam'iyyar APC ba.

Yayin jawabinsa, Daimagoro ya ce idan har mutanen Osun za su iya zaben kirista da kirista a matsayin gwamna da mataimaki, ba laifi bane idan an yi hakan a matakin zaben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164