Hotunan Lokacin da Gwamna Hope Uzodinma Na APC Ya Karbi Bakuncin Peter Obi
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya dura jihar Imo domin gudanar taron gangamin kamfen
- Obi, wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne ya samu tarbar gwamnan APC, Hope Uzodinma na jihar ta Imo
- Gwamnan jijar Imo ya yiwa Obi tarba mai kyau, lamarin da ya nuna abota da aminta tsakaninsu ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba
Owerri, jihar Imo – Gwamnan jihar Imo, Hop Uzodinma ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi a ranar Talata 6 Disamba, 2022 don fara gangamin kamfen a jihar.
Gwamna Uzodinma da Obi sun yi gaisuwar da ke nuna abota da aminci yayin da dan takarar na Labour ya sauka a filin jirgin Mbakwe da ke birnin Owerri na jihar.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta ce, gwamna Uzodinma ya karbi Obi ne a matsayin aboki duk da kuwa suna da bambacin ra’ayin siyasa.
Uzodinma dai shine gwmanan Imo mai ci, kuma yana mulki ne a karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Meye karbar da Uzodinma ya yiwa Obi ke nufi?
Sanarwar ta bayyana cewa, tarbar da Uzodinma ya yiwa Obi ba komai bace face ta abota, kuma zai iya yiwa kowa ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, a ranar Lahadi 4 ga watan Disamba gwamna Uzodinma ya sake jaddada matsayarsa cewa, kofarsa a bude take ga kowa ba tare da duba ga jam’iyyar da suke bi ba.
Kalli hotunan:
Martanin jama'a a shafin Facebook
Jama'a da dama sun yi martani mai dumi a shafin Facebook bayan da suka ga yadda gwamnan ya karbi bakuncin Peter Obi.
Bren SimVal Mann yace:
"Haka abin yake. Ba komai bane, watannin baya Charles Soludo ya yi irin wannan kyakkyawar tarba ga Mr Peter Obi. Meye ya yi bayan haka?
"Gaskiyar itace, talakawa ne za su tantance a zaben 2023."
Obinna Kesta Anum yace:
"Gwamna Uzodinma cikakken dan dimokradiyya ne kuma yana ci gaba da nuna hakan. Allah ya yi masa albarka uya ci gaba da daidaita hanyar Mr Obi."
Emmanuel Offurum yace:
"Ina son wannan, amma babu wanda ya san abin da ke cikin zukatansu. Allah ne kadai masani. 'Yan siyasa na da wayo wajen wasa da kuma tafiyar da bukatunsu."
A baya dan takarar NNPP ya bayyana cewa, yana da lafiya kuma yana tabbaci kan lafiyarsa daga yanzu zuwa nan da shekaru 30.
Kwankwaso ya ce kowane dan takarar shugaban kasa ya kamata ya nuna shaidar lafiya.
Asali: Legit.ng