Ina da Tabbacin Lafiya Ta Daga Yanzu Har Nan da Shekaru 30, Inji Dan Takarar Gaje Buhari, Kwankwaso
- Dan takarar shugaban kas ana jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana tabbacin lafiyarsa ga ‘yan Najeriya
- A wani rubutun Twitter, Kwankwaso ya ce sakamakon gwajin lafiyarsa na karshe ya nuna yana da 'Guarantee' na lafiyarsa daga yanzu zuwa shekaru 30
- Tsohon gwamnan na jihar Kano ya kalubalanci sauran ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 su nuna sakamakon gwajin lafiyarsu ga ‘yan kasar
Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ya bayyana kwarin gwiwarsa game da lafiyar jikinsa.
Kwankwaso ya bayyana halin da yake ciki na koshin lafiya a shafin Twitter a ranar 6 ga watan Disamba, inda yace binciken lafiya ya nuna lafiyarsa kalau sai godiyar Allah.
Kwankwaso ya ce daga sakamakon gwajinsa, likitoci sun ba shi tabbacin kasancewa cikin koshin lafiya daga yanzu zuwa shekaru 30.
Jigon siyasan na Arewa ya bayyana hakan ne tare da yin sharhi da cewa, ya wajaba kan duk wani dan takara ya sanar da ‘yan Najeriya halin lafiyarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Kwankwaso a shafin Twitter:
“Na yi imani da cewa idan kana son mulkar jama’a, suna binka bashin sanin gaskiya game da halin lafiyarka.
“Ina mai tabbatar muku da cewa ina cikin koshin lafiya zan kuma iya bayyana takardar shaida a gare ku ku gani. Kuma gwajin lafiya da na yi a baya-bayan nan ya ba ni tabbacin shekaru 30."
Kwankwaso ya gana da jiga-jigan gwamnatin Amurka
A bangare guda, Kwankwaso ya gana da jiga-jigan ma’aikatan gwamnatin kasar Amurka a ranar Alhamis 1 ga watan Disamba.
Wannan na fitowa ne daga bakin wani hadiminsa, Hon. Saifullahi Hassan a shafinsa na Twitter.
Hassan ya yada hotunan lokacin da Kwankwaso ke sauka a Amurka domin ganawa da wadannan manyan jiga-jigan kasar waje.
Atiku ya fi Tinubu alheri ta fuskoki da yawa, ya lissafo dalilai
Wani jigon siyasa a kasar nan ya bayyana cewa, Atiku ba sa'an Tinubu bane idan ana maganar cancanta da nagarta mai kyau.
Ya bayyana hakan ne tare da bayyana dalilansa da cewa, Atiku bai da wani abin da ake tuhumarsa a kai a tarihinsa.
Ya kuma shaida cewa, kowa ya san silar tara kudin Atiku sabanin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng