Yaushe Zaka Fara Tsayuwa Kan Zantukanka? Gwamna Wike Ya Caccaki Yakubu Dogara

Yaushe Zaka Fara Tsayuwa Kan Zantukanka? Gwamna Wike Ya Caccaki Yakubu Dogara

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya caccaki Yakubu Dogara bayan ya ga kwatsam ya koma goyon bayan Atiku Abubakar, ’dan takarar PDP
  • Wike yace abu daya da baya iya jurewa shi ne ganin mutum maras dabi’a wanda baya iya tsayuwa kan kalamansa komai kuwa muhimmancinsu
  • Gwamnan Ribas din yace Dogara yana gaba-gaba wurin goyon bayan a mika takarar shugabancin kasa hannun Kudu amma yanzu ya koma wurin ‘dan arewa

Ribas - Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas ya caccaki Yakubu Dogara, tsohon kakakin majalisar wakilai kan bayyana goyon bayansa ga takarar Atiku Abubakar, jaridar TheCable ta rahoto.

Gwamna Nyesom Wike
Yaushe Zaka Fara Tsayuwa Kan Zantukanka? Gwamna Wike Ya Caccaki Yakubu Dogara. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

A ranar Juma’a, Dogara da wasu shugabannin addini na arewacin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar inda suke ce shi ne zabi mafi inganci a cikin sauran ‘yan takaran shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya Ya Fice Daga APC, Ya Koma PDP

A yayin jawabi a ranar Litinin yayin kaddamar da titin Indorama zuwa Agbonchia Ziegler an Ogale zuwa Ebubu ta gabas, Wike ya bayyana fusatarsa kan wannan goyon bayan.

Gwamnan jihar Ribas din yace Dogara yayi ikirarin cewa yana son a kai takarar shugabancin kasa zuwa kudu amma yanzu ya juya yana goyon bayan ‘dan arewa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Abinda na tsana a rayuwar nan shi ne mutanen da basu da dabi’a. Ba zan iya jurewa ba. Idan lokacin da ya kamata yayi, zan kalubalancesu mu yi muhawara.”

- Wike yace.

“Tambaya Dogara dalilinsa na barin PDP. Mun yi zamu hadu da Dogara. Kawai sai ya kawo uziri, kwatsam na gan shi a TV Shugaba Buhari yana karbarsa ya koma APC.
“Nace babu matsala. Dogaran da ake magana shi ne yace a mika shugabancin kasa ga Kudu saboda a samu zaman lafiya. Yanzu na ji wannan Dogaran yana goyon bayan Atiku wanda kuma ‘dan arewa ne. Haka kake lamurran ka? Me yasa baka magana ka tsayu a kanta?”

Kara karanta wannan

‘Yan Tinubu Sun Ambaci Jihar Arewa 1 da Za Tayi Wa Atiku Nisa, APC Za Tayi Galaba

- Ya kara da cewa.

A ranar Lahadi, ofishin yada labaran Peter Obi, ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar LP suka caccaki Dogara kan goyon bayan Atiku.

Obi ya zargi Dogara da zama bakin ganga kuma sun ce ya tafka babban kuskure.

Yakubu Dogara ya sauya sheka

A wani labari na daban, tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya koma jam’iyyar PDP inda ya fita daga ta APC.

Wannan na zuwa ne bayan kwana daya da kwatsam ya koma goyon bayan Atiku Abubakar ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel